Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sanarwar fadar Shugaban Nijeriya ta ce yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Hukumar Tara Harajin Kasar, FIRS da wani kamfanin Faransa damar ganin bayanan masu biyan harajin Nijeriya ko manhajar int.
Gwamnatin Nijeriya ta mayar da martani kan masu sukar wata yarjejeniya da ta ƙulla da wata hukumar ƙasar Faransa mai aikin tara haraji.
Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu na kan harkar watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya fitar da wata sanarwa da sunan Hukumar Tara Haraji ta Tarayyar Nijeriya (FIRS), inda ya ƙaryata zarge-zargen.
Sanarwar ta ce yarjejeniyar da Nijeriya ta shiga da hukumar kula da kashe kuɗaɗe da tara haraji hukumomin Faransa (DGFiP), ta taƙaita ne kan taimakon fasaha da horaswa da takwarorinsu na Nijeriya.
A saƙon da Onanuga ya wallafa a shafinsa na X mai ɗauke da sa-hannun hukumar FIRS, ya ce yarjejeniyar ba za ta bai wa Faransa damar ganin bayanan masu biyan harajin Nijeriya ko manhajar intanet ɗin ƙasar ba.
“Hukumar NRS, kamar hukumar da ta gabace ta FIRS, tana fifita tsaron ƙasa da kuma gindaya sharruɗa masu ƙarfi wajen kare bayanan masu biyan haraji,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwa ta ce hukumomin tara haraji a faɗin duniya suna shiga irin wannan yarjejeniyar domin inganta aiki, tare da musayar ilimi da kuma rungumar tsare-tsaren da suka fi dacewa a duniya.
Manufar yarjejeniyar
“Hukumar DGFiP tana cikin hukumomin harajin da suka fi fice a duniya, inda take da ƙwarewa ta fiye da shekaru 100 da kuma ƙwarewa a sauyin fasahar dijital da yi wa masu biyan haraji hidima da gwamnati da kuma tafiyar da kuɗaɗen gwamnati,” in ji sanarwar.
“Wannan haɗin-gwiwar ya bai wa Nijeriya damar koyi daga wannan ƙwarewar. [Tallafin] na shawara ne ba na kutse ba, kuma yana ƙarƙashin cikakken ikon Nijeriya. Saɓanin rashin fahimta, yarjejeniyar ba ta kawar da ayyukan masu ba da fasaha na cikin gida ba”.
Kazalika sanarwa ta ce hukumar FIRS da hukumar NRS da za ta maye gurbinta na ci gaba da aiki tare da masu kamfanonin fasaha na Nijeriya irin su NIBSS da Interswitch da PayStack da kuma Flutterwave.
a ƙarshe, sanarwar ta ce hukumar tana maraba da muhawarar jama’a game da gyara dokar haraji, tana mai cewa sai dai kuma ya zaman wajibi muhawarar dole ta mayar da hankali kan asalin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa da maƙasudinta.
Maimakon yin zagon ƙasa ga ‘yancin kan Nijeriya, sanarwar ta ce yarjejeniyar tana ƙarfafa shi ne ta hanyar taimakawa wajen gina tsarin haraji mafi inganci a duniya, wanda ke da cikakken iko kan tsare-tsarensa.
Comments
No comments Yet
Comment