Kwamitin zai haɗa hukumomin gwamnati da kamfanonin mai waɗanda za su lalubo hanyoyin magance matsalolin da ke kawo cikas ga samarwa da jigila da kuma rarraba fetur da dizal da iskar gas.
Gwamnatin Nijar ta kafa wani kwamitin domin magance matsalolin samar da man fetur da ƙara yawan tace ɗanyen mai a cikin gida da kuma warware basussukan da ke tsakanin gwamnati da masu gudanar da ayyukan ɓangaren man fetur cikin watanni uku.
An ƙaddamar da kwamitin ne ranar Litinin, 12 ga Oktoba, a ofishin Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Nijar (ANP).
Kwamitin zai haɗa hukumomin gwamnati da kamfanonin mai waɗanda za su lalubo hanyoyin magance matsalolin da ke kawo cikas ga samarwa da jigila da kuma rarraba fetur da dizal da iskar gas da ake amfani da shi wajen girke-girke a gida (LPG).
Ana kuma sa ran kwamitin zai taimaka wajen ƙara yawan ɗanyen man da matatar mai ta Zinder, wadda kamfanin Société de Raffinage de Zinder (SORAZ) ke tacewa daga ganga 15,000 zuwa ganga 20,000 a kowace rana, tare da haɗin gwiwar kamfanin China National Petroleum Corporation Niger Petroleum.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin matsin lamba kan tsarin samar da man fetur a Nijar.
Ministan Man Fetur, Hamadou Tini, ya ce ƙasar ta fuskanci ƙarancin fetur na lita miliyan 196.62 da dizal da ya kai lita miliyan 52.60 a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2026.
Kwamitin zai sake duba basussukan da ke tsakanin gwamnati da Kamfanin albarkatun Man Fetur na Nijar (SONIDEP) da matatar SORAZ da kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasa NIGELEC da kuma CNPC Niger Petroleum.
Haka kuma, zai tsara yadda za a biya basussukan, inda za a ba da fifiko ga bashin da gwamnati ke bin SONIDEP da kuma wanda SONIDEP ke bin matatar mai.
Hukumomi sun umarci kwamitin da ya riƙa sa ido a kullum kan yawan man fetur da ke ajiye da kuma wanda ake shigar da shi ƙasar.
Za kuma a riƙa tsara shirin samar da man fetur na kwanaki 30 a kowane lokaci, tare da samar da matakan hana ci gaba da taruwar basussuka.
Kwamitin zai kuma tsara hanyoyin tabbatar da samar da isasshen dizal ga tashoshin samar da wutar lantarki ta hanyar zafi, tare da nazarin wasu hanyoyin rage dogaro da dizal.
Firaministan Nijar Lamine Zeine ne zai jagoranci kwamitin wanda ya ƙunshi mataimakansa huɗu da suka hada da Ministan Man Fetur da ministan Tattalin Arziki da Kuɗi da Ministan Kasuwanci da Masana'antu da kuma Ministan Shari'a.
Kazalika kwamitin zai yi aiki na tsawon watanni 12 da farko kana ana iya tsawaita wa’adinsa har sai an kammala gyaran matatar mai tare da dawo da samar da man fetur yadda ya kamata.
Gwamnatin ta ce ana sa ran matakan za su inganta samar da man fetur a faɗin ƙasar, tare da kiyaye farashin da gwamnati ta kayyade a gidajen mai da kuma ƙarfafa dorewar kuɗaɗen gudanar da ayyukan ɓangaren man fetur.

