Zamfara, wadda aka sani da arzikin zinari, ta fara samun barkewar cutar gubar dalma a shekarar 2010.

Gwamnati ta kori masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a Zamfara kan ɓarkewar cutar gubar dalma

Gwamnatin Nijeriya ta umarci masu haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da su gaggauta barin duk wuraren haƙar ma'adinai a jihar Zamfara da ke arewa maso yamma, bayan tabbatar da ɓarkewar cutar gubar dalma.

Ministan Raya Ma'adanai, Dakta Dele Alake ne ya bayar da wannan gargaɗi a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Segun Tomori, ya fitar a ranar Talata a Abuja, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito.

Zamfara, wadda aka sani da arzikin zinari, ta fara samun barkewar cutar gubar dalma a shekarar 2010.

Wannan barkewar cutar ta samo asali ne daga ayyukan hakar zinari na gargajiya, wanda ya haifar da gurbacewar muhalli sannan ɗaruruwan mazauna yankin da dama suka kamu da cutar gubar dalma.

Dakatar da haƙar ma'adinai

Alake ya bayyana cewa ba za a cigaba da duk ayyukan hakar ma'adinai har sai an fitar da Ka'idojin Gudanarwa (SOP) da za su jagoranci cigaba da bincike a jihar.

Ya nuna damuwa cewa haramcin haƙar ma'adinai na tsawon shekaru shida a jihar, wanda aka ɗage a watan Disamba 2024, ya kamata ya hana duk wani lamari na yaɗuwar gubar dalmar nan. An ruwaito sabuwar ɓarkewar cutar a yankin Bungudu na jihar.

“Wannan barkewar cutar shaida ce cewa cibiyoyin gargajiya da na yankin sun bari masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba su gudanar da ayyukansu a yankunansu, suna take dokar haramcin,” in ji shi.

“Kowane ɗan ƙasa ya kamata ya bi dokoki da ƙa'idojin da hukumomin da aka kafa suka tsara.

Cibiyoyinmu na gargajiya masu daraja da hukumomin yankuna, waɗanda ake biya daga asusun tarayya, suna da babban nauyi wajen tabbatar da bin umarnin gwamnati,” in ji hukumomin.

“Duk da haka, inda suka nuna halin ko-in-kula da kuma watsi da nauyin da ke kansu, suna haifar da yanayin rashin doka wanda ke da mummunan sakamako, kamar yadda muke gani a wannan yanayin,” in ji shi.

A cewarsa, masana da rahotannin ma'aikata za su bayar da shawarwari na musamman don taimaka wa gwamnati wajen hana irin wannan bala'i a nan gaba.

#