Shugaba Mahama ya ɗauki matakin nan-take domin kare gaskiya

An kira jakadan Ghana a Nijeriya gida kan zargin maguɗin zaɓe

Shugaban ƙasar Ghana, John Mahama, ya yi wa jakadan ƙasar a Nijeriya, Baba Ahmed, kiranye bisa zargin hannu a maguɗin zaɓe a zaɓen fid da gwani na ‘yan majalisu a mazaɓar Ayawaso East. TRT Hausa

Wata sanarwa da fadar Shugaban ƙasar ta fitar a Accra ta ce an yi kiranyen ne saboda rawar da ake zargin Ahmed ya taka a maguɗin zaɓen, duba da kasancewarsa jami’in gwamnati kuma mai neman takara. TRT Hausa

Sanarwar ta ƙara da cewa matakin ya fara aiki nan take, domin kauce wa duk wani zargin rashin adalci ko saɓa wa dokokin ɗa’ar ma’aikatan da ke riƙe da muƙaman siyasa. TRT Hausa

Ta jaddada cewa ci gaba da zamansa a ofishin abu ne da ba zai yiwu ba a irin wannan yanayi.

An zargi masu neman takara a zaɓen fid da gwani da laifin sayen ƙuri’u.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#