Sport
Dollar
42,6137
0.03 %Euro
50,1966
0.66 %Gram Gold
5.843,6800
0.87 %Quarter Gold
9.503,9100
-0.01 %Silver
86,9600
2.76 %Ghana ta ce an tsare matafiya bakwai 'yan Ghana ba tare da wani dalili ba bayan isarsu Tel Aviv ranar Lahadi. Daga cikinsu akwai mambobi hudu na tawagar 'yanmajalisa da suka halarci taron shekara-shekara na tsaron intanet na kasa da kasa.
Gwamnatin Ghana ta yi Allah wadai da ƙaƙƙarfar murya ga Isra'ila bayan abin da ta kira "wulaƙanci da cin mutuncin" da aka yi wa matafiya 'yan Ghana a filin jirgin saman Ben Gurion da ke Tel Aviv.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana ta ce ta "kaɗu" da halayen hukumomin Isra'ila, tana mai cewa tun daga ranar Lahadi, 7 ga Disamban 2025, an "kai wa 'yan Ghana da suka isa Isra'ila hari da gangan" don yin bincike mai tsauri da rashin adalci.
A cewar sanarwar, an tsare matafiya bakwai 'yan Ghana ba tare da wani dalili ba bayan isarsu ranar Lahadi. Daga cikinsu akwai mambobi hudu na tawagar 'yanmajalisa da suka halarci taron shekara-shekara na tsaron intanet na kasa da kasa da aka yi a Tel Aviv.
An ruwaito cewa an sake su ne bayan shafe fiye da sa'o'i biyar da abin da Ma'aikatar ta bayyana a matsayin "tsauraran matakan diflomasiyya."
An tasa ƙeyar sauran matafiya ukun a wani jirgin don mayar da su gida, kuma tun daga lokacin sun koma Ghana.
“Gwamnati ta yi Allah wadai da abin da jami'an Isra'ila suka yi a matsayin nuna wariya, wulakanci, da rashin daidaito da dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu,” in ji sanarwar.
Ghana da Isra'ila sun shafe fiye da shekara 60 suna hulɗar diflomasiyya, tare da tafiye-tafiye masu yawa tsakanin 'yan ƙasashen.
Ma'aikatar Harkokin Waje ta yi watsi da hujjojin da Isra'ila ta bayar - cewa Ofishin Jakadancin Ghana da ke Tel Aviv bai ba da hadin kai game da tsarin korar 'yan kasar ba - a matsayin "abin da ba za a iya amincewa da shi ba kwata-kwata," tana mai dage cewa ofishin ya yi aiki yadda ya kamata bisa ga dokokin kasa da kasa kuma ya amsa buƙatun Isra'ila.
Ana sa ran Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana za ta gayyaci jami'an Ofishin Jakadancin Isra'ila da ke Accra a yau don su karɓi ƙorafi da tur ɗin da Ghana ta yi da lamarin a hukumance.
A halin yanzu, Gwamnatin Ghana ta ce tana la'akari da "daukar matakin da ya dace na mayar da martani."
Ma'aikatar ta watsa sanarwar ga dukkan gidajen watsa labarai kuma ta yi kira ga jama'a da su kwantar da hankali yayin da ake ci gaba da gudanar da harkokin diflomasiyya.
Comments
No comments Yet
Comment