Wannan taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kira kan sojojin majalisar su bar kasashe da dama na nahiyar.

Ghana na karbar bakuncin taron MDD kan aikin sojojin wanzar da zaman lafiya

Ghana na karbar bakuncin taron kwana biyu kan aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka.

Wannan taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kira kan sojojin majalisar su bar kasashe da dama na nahiyar.

Ministoci da wakilai daga kasashe 85 suna gudanar da taron a Accra babban birnin Ghana daga 4 ga watan Disamba zuwa biyar ga watan na Disamba.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ana yin wannan taron ne “domin samun goyon baya da kuma samun sadaukarwa domin karfafa ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD domin shawo kan kalubalen da ake fama da su a yanzu da na nan gaba.”

Mali da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Sudan su ne kasashen Afirka na baya-bayan nan da suke neman Majalisar Dinkin Duniya ta janye dakarunta inda suke cewa ba su da wani amfani tare da musu zargin take hakkin bil’adama.

Samar da zaman lafiya

A Mali, tuni dakarun na MDD suka soma janyewa inda a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo kuwa, gwamnatin kasar da MDD sun amince tare da cimma matsaya kan janye dakarun.

A al’adance ana tura sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasashen da suke samun rashin zaman lafiya.

Babban aikinsu a kowace kasa suka je shi ne kwantar da tarzoma da samar da zaman lafiya.

#