A kauyen Tazlar da ke yammacin Turkiyya, al'ummu da dama sun rayu da girma ba tare da shan taba sigari ba.

Ga labarin ƙauyen Turkiyya ɗaya tilo da ya tsani shan taba sigari

Ko kana cikin wani matsattsiyar hanya mai cunkoson jama'a a Istanbul ko kuma kusa da wurin shakatawa na bakin teku a Antalya, mai yiwuwa za ka ci karo da shagon da aka rubuta "Tekel".

Wadannan shaguna na gefen titi, wadanda galibi ake musu fentin shudi a bangonsu na waje sun samo asali ne daga tsohon tsarin gwamnati na mallakar ikon sayar da taba kadai (Tekel). Wannan shi ne wurin da ake zuwa a sayi sigari.

An kafa Tekel ne a tsakiyar shekarun 1920, lokacin da sabuwar gwamnatin Turkiyya ta karbe ikon gudanar da kasuwancin taba mai matukar riba daga hannun kamfanonin kasashen waje; wadannan kamfanoni ne suka mamaye kasuwar a shekarun karshe na Daular Usmaniyya.

Tun da farko dai Turkiyya kasa ce mai noman taba. Har ma hoton rakumin da ya zama alamar sigarin "Camel" yana da asali daga Turkiyya. Kamfanin RJR na Amurka, wanda shi ne babban kamfanin da ke samar da sigarin Camel, ya yi amfani da cakudaddun ganyane taba da aka noma a Turkiyya wajen hada sigarin tasa. Saboda haka, wani ma'aikaci a sashen tallace-tallace na kamfanin ya ga ya dace a sanya hoton rakumi a matsayin tambarin kamfanin — duk da cewa ba a san Turkiyya da kasancewar wadannan dabbobi masu kumburin baya ba.

Wannan lokaci ya kasance muhimmin sauyi ga masana'antar samar da sigari a Turkiyya.

Sai dai a daidai wannan lokacin, a wani karamin kauye mai suna Tazlar da ke gundumar Sinanpasa a lardin Afyonkarahisar na yammacin Turkiyya, wani sabon sauyi na daban yana gudana.

Karkashin jagorancin wani dattijon kauye mai suna Ahmet Aga, mazauna kauyen sun dauki alkawarin daina shan taba domin zama abin koyi ga al’ummu masu zuwa.

Wannan mataki ya canza kauyen Tazlar har abada zuwa wani wuri na musamman da babu shan taba, kimanin shekaru dari kafin a fara samar da dokokin zamani na kare lafiyar jama'a.

Yanzu haka an kusa cika shekaru dari, kuma kauyen—mai yawan jama'a kimanin 2,000—har yanzu yana da suna a matsayin wurin da ba kasafai ake ganin masu shan taba ba.

Labarin Tazlar yana da matukar muhimmanci a yanzu yayin da gwamnatin Turkiyya ke kokarin rage yawan shan taba. Ankara na nazarin wata doka da za ta haramta shan taba har tsawon rayuwa ga duk wanda aka haifa bayan watan Janairun 2015.

An san Shugaba Recep Tayyip Erdogan da tsananin adawa da shan taba. An ruwaito cewa ya shawarci Firaministar Italiya, Giorgia Meloni, da ta daina shan taba, kuma ta yi hakan a farkon wannan shekarar.

Bincike daban-daban ya nuna cewa 'yan kasar Turkiyya na daga cikin mutanen da suka fi yawan shan taba sigari. Amma wannan ba matsala ba ce a Tazlar.

Ta yaya hakan ya faro

Tarihi ya manta da Ahmet Aga gaba ɗaya, kuma mazauna Tazlar ba za su iya tunawa da abin da iyayensu suka gaya musu ba.

Amma kamar yadda labarin ya nuna, Aga ya kasance yana son kare lafiyar jiki duk da ƙarancin kuɗin mutanensa. A shekarar 1928, lokacin da mutanen ƙauyen suka yi rantsuwar gama gari kan taba, Aga ya sami damar cin gajiyar lokacin da 'yan ƙauye kaɗan ne kawai ke shan taba, kuma ya yi nasarar shawo kansu su daina.

"Mun girma ba tare da mutanen da ke shan taba a kusa da mu ba," in ji Mehmet Aydogmus mai shekaru 66, wanda ke aiki a matsayin mai wa'azin ƙauye kuma akawu.

"A gaskiya dai, rashin shan taba ba shawara ce da muka yanke daga baya a rayuwa ba. Ya zama wani ɓangare kai tsaye na rayuwarmu da al'adunmu."

Wannan bambancin yana da muhimmanci wajen fahimtar ƙwarewar Tazlar.

Maimakon dogara kawai ga yanke shawara na mutum ɗaya, ƙauyen ya bayyana cewa ya haɓaka al'adar gama gari wadda shan taba ba ta taɓa zama ruwan dare ba.

Aydogmus ya ce ba a gabatar da ƙa'idar ga yara a matsayin doka da aka sanya daga sama ba. Maimakon haka, ta zama wani abu da suka runguma ta hanyar kallon iyayensu, kakanninsu da maƙwabtansu.

"A lokacin da nake yaro, ganin mutum yana shan taba a kauyenmu ba abu ne da muka saba gani ba," in ji Aydogmus yana tunawa.

Tazlar kauye ne mai gidaje da aka gina da tubali mai launin ja, kuma gonakin tumatir mai launin rawaya da amfanin gona sun zagaye shi. Mazauna kauyen suna bin tsarin rayuwa na yau da kullum: suna tashi da wuri su kuma kwanta bayan faduwar rana. A nan, kowa ya san kowa.

Rashin amincewar mazauna kauyen game da shan taba ya samo asali ne daga damuwa game da lafiya, amma Aydogmus ya ce ba za a iya bayyana wannan al'ada ta fuskar lafiya kadai ba.

"Dattawanmu suna yawan gaya mana game da illar da shan taba ke haifarwa ga lafiyar dan adam," in ji shi. "Amma ba su tsaya kawai a kan cewa yana da illa ga lafiya ba."

Sun kuma yi magana game da tasirin munanan dabi'u ga iyalai, al'umma, da kuma karfin ikon mutum na sarrafa kansa.

"Mun koyi wannan a hankali," in ji shi. "Ko a lokacin da muke yara kuma ba mu cika fahimtar ma'anarsa ba, mun san daga halayen dattawanmu cewa wannan batu ne mai muhimmanci a gare mu."

A cewar Aydogmus, tsarin da ƙauyen ke bi ya haɗa da nauyin da ya rataya kan iyali, dabi'un addini, da kuma haɗin kan al'umma.

Iyali suna kula da yaransu. Tsofaffi suna yi wa matasa gargaɗi. Maƙwabta sun san juna. Kuma ana ɗaukar ɗabi'a ba wai a matsayin lamarin mutum ɗaya kaɗai ba, a'a, a matsayin abin da zai iya shafar dukkan 'yan uwa da kuma al'umma baki ɗaya.

Idan yaro ya fara nuna wata ɗabi'a da iyali ke ganin tana da illa, 'yan uwa da maƙwabta ba sa zama suna kallo kawai ba tare da sun yi komai ba.

"Idan matashi ya yi kuskure a wani wuri, mutane ba sa cewa, 'Wannan ba abinda ya shafe ni ba ne,'" in ji Aydogmus. "Mutane suna sanin juna a ƙauyen. Kowa ya san ɗan wane ne wani, ko jikan wane ne shi."

Amma ta yaya za a kiyaye al'ada idan babu matasan da za su ci gaba da tafiya a kan tafarkin da aka shimfiɗa?

Yaduwa kamar hayaki

Murat Karasogut, mai shekaru 29, wanda ya girma a ƙauyen Tazlar, kan fuskanci yanayi mai ban mamaki dangane da bambancin al'adu duk lokacin da ya yi tafiya zuwa wasu sassan ƙasar.

"Idan muka ga mutum yana shan taba a waje, wani lokacin muna cewa, 'Ba mu da irin wannan abu a ƙauyenmu.'"

Ya ce a Tazlar, rashin shan taba shi ne abin da aka saba da shi kuma ake tsammani daga kowa. Ba sai an riƙa gaya wa matasa akai-akai su guji shan taba ba, domin tun asali shan taba ba ya cikin al'adun yau da kullum na ƙauyen.

"Rashin shan taba al'ada ce a ƙauyenmu, shi ya sa matasa ke karɓar wannan dabi'a cikin sauƙi," in ji shi.

Ya yi imanin cewa wannan bambanci yana da matuƙar muhimmanci, duk da cewa matasa na ci gaba da ganin taba a wurare daban-daban.

Sai dai, yayin da matasa da dama a Tazlar ke ci gaba da ƙaura zuwa birane, ana samun damuwar cewa tsayayyen matsayin da aka ɗauka na kin shan taba na iya raguwa ko ɓacewa a nan gaba.

Fiye da kashi biyu cikin uku na matasan ƙauyen a yanzu suna zaune a birane kamar Istanbul da Bursa, inda suka je wuraren saboda samun damar ingantaccen ilimi da kuma guraben aiki.

A ra’ayin Aydogmus da Karasogut, makomar al'adar Tazlar ta dogara ne kacokan kan ko matasan za su zaɓi ci gaba da ita ko a'a.

Karasogut ya yi imanin cewa matasa suna da wani nauyi na musamman a wannan fanni.

"Ba ma son mu zama koma baya," in ji Aydogmus. "Amma kuma ba ma son mu rasa tarihinmu ko al'adunmu na baya."

#