Alhaji Usman Baba Pategi ya taka rawa a matsayin Samanja Mazan Fama a wasan kwaikwaiyon da aka rika gabatarwa a Gidan Rediyo Nijeriya na Kaduna a shekarun 1980.
Fitaccen dan wasan kwaikwayo na Hausa Alhaji Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja ya rasu.
Bayanai daga iyalansa sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a Kaduna da ke arewacin Nijeriya.
Alhaji Usman Baba Pategi ya taka rawa a matsayin Samanja Mazan Fama a wasan kwaikwaiyon da aka kwashe shekara da shekaru ana gabatarwa a Gidan Rediyo Nijeriya na Kaduna.
An haife shi ranar 20 ga watan Mayu na shekara 1942 a Masarautar Pategi da ke Jihar Kwara.