Shuwagabannin biyu za su tattaunawa a tsakaninsu kuma za su halarci wani zama na tawagoginsu domin tattaunawa kan alaƙa tsakanin ƙasashen da kuma batutuwan da suka shafi duniya.

Firaministan Malaysia ya yi wa Erdogan tarba ta musamman

Firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya tarbi Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wani bikin da aka yi a hukumance.

A birnin Putrajaya, Erdogan da Ibrahim za su tattauna ranar Talata kuma za su halarci wata zama tsakanin tawagoginsu domin tattauna dangantaka tsakaninsu da kuma batutuwan duniya cikin har da yaƙin da ake yi a Gaza.

Bayan an yi bikin rattaɓa hannu kan yajejeniyoyi, za su halarci wani taron manema labarai.

Daga bayan, Erdogan zai gabatar da jawabi ga ƙungiyar haɗaka ta ‘yan kasuwar Turkiyya da Malaysia.

A ranar Lahadi ne dai, Erdogan ya fara wata ziyara ta kwana huɗu zuwa ƙasashen Malaysia da Indonesia da kuma Pakistan.

Ya gatabar da wani jawabi ranar Litinin a jami’ar Malaya, inda a ka ba shi digirin-digir-gir na girmamamwa.

"Duk da nesan da suke da shi daga juna, Turkiyya da Malaysia, waɗanda suke ɓangarori daban-daban na nahiyar Asia, haƙiƙa suna ƙawance, ‘yan uwa ne kuma ƙasashe ne da ke tare," in ji shi.

#