Sport
Dollar
40,4343
0.24 %Euro
47,1614
0.49 %Gram Gold
4.349,9900
0.54 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Erdogan yana ziyara a TRNC domin halartar tarukan tunawa da wannan aiki na soja da Turkiyya ta ƙaddamar domin mayar da martani ga juyin mulkin da Cyprus ta girka ta yi niyyar yi domin mayar da tsibirin ga ƙasar Girka.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a ranar Lahadi ya yi bikin Ranar Zaman Lafiya da 'Yanci a Arewacin Cyprus ta Jamhuriyyar Turkiyya (TRNC), yana murnar cika shekara 51 da Aikin Zaman Lafiya na Cyprus da aka ƙaddamar a shekarar 1974.
Erdogan yana ziyara a TRNC domin halartar tarukan tunawa da wannan aiki na soja da Turkiyya ta ƙaddamar domin mayar da martani ga juyin mulkin da Cyprus ta girka ta yi niyyar yi domin mayar da tsibirin ga ƙasar Girka.
Yayin da yake taya al’ummar Turkawan Cyprus murna da zuciya ɗaya, Erdogan ya rubuta a shafin X cewa: “A cikar shekara 51 da fara Aikin Zaman Lafiya na Cyprus, ina tuna shahidanmu da girmamawa waɗanda suka sadaukar da rayukansu don gwagwarmayar wanzuwar al’ummar Turkawan Cyprus, kuma ina miƙa godiyata ga tsoffin jaruman sojojinmu.”
Matsalar da ta jima tana ci gaba
Tsibirin Cyprus ya jima yana fama da rikicin da ya shafi ‘yan Cyprus na Girka da da ‘yan Cyprus Turkawa, duk da ƙoƙarin diflomasiyya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi don cim ma matsaya mai ɗorewa.
Hare-haren ƙabilanci da suka fara tun farkon shekarun 1960 sun tilasta wa Turkawa na Cyprus janyewa zuwa wasu yankuna don kare kansu.
A shekarar 1974, juyin mulkin Cyprus ta Girka da aka yi da nufin haɗa tsibirin da Girka ya sa Turkiyya ta yi amfani da soja don kare Turkawa na Cyprus daga tsangwama da tashin hankali. Sakamakon haka, aka kafa TRNC a shekarar 1983.
An samu ci gaba da ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a 'yan shekarun nan, ciki har da yunƙurin da ya gaza a shekarar 2017 a Switzerland ƙarƙashin jagorancin ƙasashen da suka kasance garanto, wato Turkiyya, Girka, da Birtaniya.
Gwamnatin Cyprus ta Girka ta shiga cikin Tarayyar Turai a shekarar 2004, shekarar da ƙasar ita kaɗai ta hana shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na kawo ƙarshen wannan rikicin da ya daɗe.
Comments
No comments Yet
Comment