Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke Chadi sun ce dubban mutane sun yi kokarin shiga kasar amma dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun hana su.

Dubban mutane sun tsere daga gidajensu a yayin da ake ci gaba da kashe-kashe a Darfur

Dubban 'yan kasar Suda suna tserewa daga Yammacin Darfur zuwa kasar Chadi a yayin da ake bayar da rahotannin kazamin ba-ta-kashi inda dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kwace iko da babban sansanin sojojin da ke El Geneina, babban birnin yankin.

Kungiyar bayar da agaji ta likitoci MSF ta ce an samu karuwar dimbin 'yan gudun hijira da ke ci gaba da kwarara cikin Chadi a kwanaki uku na farko watan Nuwamba inda kimanin mutum 7,000 suka shiga kasar. Galibinsu mata da kananan yara ne, kuma sun bayyana yadda rikicin ya yi mummunan tasiri kan fararen-hula.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke Chadi sun ce dubban mutane sun yi kokarin shiga kasar amma dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun hana su ind suka bukaci su ba su kudi.

Ranar Talata, wani jarida na kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ga jerin gwanon maza daga Darfur su nufi yankin Adre na Chadi, mai nisan kilomita 27 daga yamacin El Geneina.

Mun ga yadda ake kashe-kashe

Uku daga cikin mutanen da suka tsere sun ce sun ga yadda dakarun RFS suke kashe mutane sannan an yi zargin cewa suna far wa 'yan kabilar Masalit a garin Ardamata, wani yanki na El Geneina da ke da sansanin soji kana sun addabi sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin.

RSF ba ta ce komai a kan wannan zargi ba duk da bukatar hakan da aka mika mata. Reuters bai tabbatar da abin da ya faru ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton yadda tsakanin watan Afrilu da Yuni na wannan shekarar, dakarun RSF da mayakan sa-kai masu goyon bayansu suka kwashe makonni suna kai hari a Masalit a yayin da ake fafatawa tsakanin RSF da sojojin Sudan.

#