Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa manufofin zamantakewa da shirin ci gaban ɗan'adam na gwamnatin Jihar Kano, da nufin rage ɗawainiyar tattalin arziki da ta yi wa jihar katutu.

Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano a fannin lafiya da taimakon marasa galihu

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa manufofin zamantakewa da shirin ci gaban ɗan'adam na gwamnatin Jihar Kano, da nufin rage ɗawainiyar tattalin arziki da ta yi wa jihar katutu.

Dangote ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Jihar Kano, a ranar Juma’a, inda ya ce ya yi amanna talaka na cikin ƙunci kan halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.

Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano don inganta kiwon lafiya da ilimi da karfafa wa masu karamin karfi da ke gwagwarmayar rayuwa.

“Da farko dai mun zo nan ne don mu taya ku murnar nasarar da kuka samu a Kotun Ƙoli, ina so in tabbatar muku da goyon bayanmu a tsawon mulkin ku, watakila ba shekara hudu kawai ba amma shekaru takwas.

#