Sport
Dollar
41,1517
0.25 %Euro
48,0010
-0.21 %Gram Gold
4.509,4600
0 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%'Yan bindiga kusan 300 ne suka yi yunƙurin kutsawa ƙauyen Kumbashi da misalin karfe 3 na ranar Talata amma jami'an rundunar soji da na rundunar farin kaya ta DSS sun tunkare su, in ji shugaban Majalisar jihar ta Neja.
Jami’an tsaro a Jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga aƙalla 50 a wani ƙazamin artabu da aka yi a ƙauyen Kumbashi da ke ƙaramar hukumar Mariga.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar ta Neja, Abdulmalik Mohammed Sarkin-Daji ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba a Minna.
A cewarsa, 'yan bindiga kusan su 300 ne suka yi yunkurin kutsawa cikin al'ummar da misalin karfe 3 na rana a ranar Talata amma rundunar Sojoji da ta jami’an rundunar farin kaya ta DSS sun tunkare su.
Ya bayyana cewa maharan sun kai hari ne a sansanin jami’an DSS da ke yankin, amma jami’an tsaro sun yi arangama da su lamarin da ya yi sanadin mutuwar maharan da dama, yayin da sauran suka tsere ɗauke da munanan raunuka.
Comments
No comments Yet
Comment