Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Abderaman Koulamallah shi ma a ranar Laraba ya sake sabunta kiran da al'ummar kasar ke yi ga kasashen duniya da su ƙara zage damtse wajen tallafa wa ayyukan yaƙi da ta'addanci a yankin.
A ranar Laraba gwamnatin kasar Chadi ta lashi takobin kakkaɓe ayyukan Boko Haram, biyo bayan wani kazamin harin da mayakan ƙungiyar suka kai wani barikin sojin kasar a karshen mako.
Mayakan Boko Haram sun kashe kusan sojoji 40 tare da raunata wasu da dama a wani samame da suka kai ranar Lahadi a wani sansanin da ke yankin Tafkin Chadi, inda ake fama da kungiyoyi daban-daban masu dauke da makamai.
A martanin da ta mayar, Chadi a ranar Litinin ta ƙaddamar da harin Operation Haskanite, "da nufin tabbatar da zaman lafiyar al'ummarmu" har ma da "farauta da kawar da ƙungiyar Boko Haram da matsalolinta da masu alaƙa da ita", kamar yadda Firaminista na wucin gadi Abderahim Bireme Hamid ya shaida wa 'yan jarida a N'Djamena.
Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Abderaman Koulamallah shi ma a ranar Laraba ya sake sabunta kiran da al'ummar kasar ke yi ga kasashen duniya da su ƙara zage damtse wajen tallafa wa ayyukan yaƙi da ta'addanci a yankin.
A yankin mai yalwar ruwa da fadamu, tsibiran yankin Tafkin Chadi marasa adadi sun zama maɓoya ga kungiyoyin masu ikirarin jihadi, irinsu Boko Haram da kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP), wadanda ke kai hare-hare akai-akai kan sojojin kasar da ma fararen hula.
Kungiyar Boko Haram ta fara ƙaddamar da hare-hare a Nijeriya a shekara ta 2009, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum fiye da 40,000 tare da raba miliyan biyu da muhallansu, kuma ƙungiyar ta yaɗu zuwa ƙasashe maƙwabta.
A watan Maris din shekarar 2020, sojojin ƙasar Chadi sun yi asara mafi girma ta kwana guda a yankin, lokacin da sojoji kusan 100 suka mutu a wani samame da suka kai a gabar Tafkin Bohoma.
Gwamnati, kamar yadda ta yi a wancan lokacin, ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa daga ranar Talata, tare da yin ƙasa-ƙasa da tutoci da kuma haramta bukukuwa.