A 2018, shafin wallafa bidiyo a intanet na YouTube ya fito da wani tsari da nufin ƙarfafa bayyana gaskiya ga masu amfani da shafin.

Cewa USAID tana bai wa BBC kudi babban abin zargi ne

Daga Mazhun Idris

A 2018, shafin wallafa bidiyo a intanet na YouTube ya fito da wani tsari da nufin ƙarfafa bayyana gaskiya ga masu amfani da shafin.

Wannan fasalin ya ba wa shafin damar nuna idan bidiyon da aka wallafa a shafin an "yi shi ne da kuɗin al'umma ko na gwamnati".

Idan wani da ya yi amfanin da irin wannan kuɗn ya ɗora bidiyo, ya kamata a ga wata sanarwa ta fito a ƙasan bayan taken bidiyon. Sanarwar za ta ƙunshi mahaɗin da zai kai ka ga shafin kafar sadarwar da ta wallafa da ke Wikipedia.

Alal misali, a ƙarƙashin bidiyon da kafa kamar BBC ta wallafa, wata sanarwa za ta bayyana mai cewa, "BBC kafar Burtaniya ce mallakin gwamnati."

Sanarwar takan kuma fito a duk wata wallafa da wasu kafafen sadarwa na gwamnati suka saka.

Sauran shafukan sada-zumunta kamar Facebook sun fito da irin wannan tsarin na sanarwa tun a 2019, wadda nufinta shi ne bambance kafofin da "gwamnatoci ke iko da su ɗungurungun ko wani ɓangare".

Wani hanzari shi ne idan ka buɗe bidiyon shafin cibiyar "BBC Media Action" na YouTube, wadda wani shiri ne na ayyukan jin-ƙai da cigaba wanda BBC ta assasa a 1999, ba za ka ga irin sanarwar da ke cewa da kuɗin jama'a aka yi shirin ba.

Matsalar karɓar kuɗi

Ranar 2 ga Fabrairun, babban abokin shugaban Amurka, Donald Trump wanda ya mallakin shafin X, wato Elon Musk, ya wallafa a shafinsa cewa cibiyar USAID ta yi ta amfani da dalolin al'umma wajen biyan "kafofin yaɗa labarai don su wallafa farfaganda".

Elon Musk ya jaddada zarge-zargen nasa bayan kwanaki huɗu, inda ya ambaci suna. "Me ya sa ake amfani da kuɗin al'ummar Amurka wajen ɗaukar nauyin BBC?".

Shugaba Trump ya biye wa Musk, inda ya zargi USAID da bai wa gidajen jaridu kuɗi don fifita jam'iyyar Democratic Party.

Kakakin BBC Media Action ya yi bayani ga Reuters cewa duk da cibiyar tana karɓar kuɗi daga USAID da sauran masu ba da kuɗi, shirin wani ɓangare ne kawai na jin-ƙai na BBC, kuma yana "cin gashin-kansa da ba shi da alaƙa da kafar labarai ta BBC".

A wata sanarwar yaɗa labarai ta yi iƙirarin cewa "BBC Media Action shiri ne da ke tallafa wa gidajen jaridu na ƙasashen duniya don isar da amintattun bayanai ga al'ummar da ke buƙata".

Rasa kima

Yayin da badaƙalar USAID da BBC ke fitowa fili, akwai ƙarin damuwa kan yadda ake sauya fahimtar mutane da amfani da kuɗaɗe don yaɗa farfaganda.

Ƙasshen Afirka sun fi samun cutuwa daga irin wannan tsari na nuna fifiko.

Wani marubuci kuma mai shirya fina-finai ɗan Ghana, Dwomoh-Doyen Benjamin ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "To wa yake fayyace mene ne 'amintattun bayanai' — masu ba da ƙudin ko kafofin yada labaran?".

Benjamin, wanda shugaban African Chamber of Content Producers ne, ya ce, "Waɗanannan bayanai na abin kunya sun fito da munafurcin da kafafen sadarwa na Yammacin duinya ke yi wajen saka-ido kan ayyukan jarida a duniya, musamman a Afirka.

Babbar tambayar ita ce: Shin gwamnatin Amurka ta ɗauki nauyin babbar kafar watsa labarai ta Burtaniya, ko a'a?

Idan BBC ta iya gujewa alhakin "taimakawa kisan-kiyashin Isra'ila a Gaza", shin shugabannin BBC sun amsa cewa sun rasa aminci saboda cakwakiyar farfagandar manufofin diflomasiyya?

Girman ɓarna

Gwada cire suna BBC, sannan ka saka sunan wata kafar yaɗa labarai ce ta jama'a a wata ƙasa mai tasowa, aka ce ana zargi da karɓar kuɗi daga gwamnatin wata babbar ƙasa.

Iƙirarin da za a yi shi ne cewa an samu wadatattun hujjojin da ke nuna cewa ayyukan watsa labarai na kafar ya zama mai nun son-kai kuma mara aminci.

Sauya tunani a ɓoye

Wani abin lura shi ne, farfaganda a salo guda ne da ita ba, wanda yake taƙaita a ɗakuna watsa labaraia kawai.

Ana iya isar da farfaganda a duka ayyuka gidajen talabijin jarida — kama daga sharhin labarai da tsarin yin labarai da tsara shirye-shirye.

Ana iya murɗa tunanin al'umma ta hanyar zaɓar bayanan da ake fitowa da su, da zaɓar mahanagr da ake jaddadawa, da kawar da wasu bayanai, da shirya batutuwa, da tayar da tsana, da assasa soyayya, da rufe baki , ko hana wasu magana.

A tsarin zamani da ake amfani da jarida a matsayin makami, yaɗa labaran ƙarya ba ya tsayawa kan yaɗa ƙarya kawai don ɓata suna.

Yaɗa bayanan ƙarya wani makami ne mai ƙarfi, haka ma salon ba da fifiko kan wani abu ko yawan maimaita wasu zaɓaɓɓun bayanai ko mahanga.

Masana cigaban duniya suna nuni da cewa, ana yawan amfani da shirye-shirye masu zummar jin-ƙai don kau da ido daga shirye-shiryen leƙen-asiri, wanda ake yi don yaudarar masu amfana domin cim ma wasu manufofi.

Misali, ƙungiyoyin masu ba da tallafin kuɗi ba lallai su nemi yin iki na kai-tsaye da shirin da suke ɗaukar nauyi ba, matuƙar dai an shigar da ajandarsu cikin ƙa'idojin yarjejeniyar samar da kuɗin.

Ko ma mene ne, irin wannan ajandojin ba sa daidai da tsarin tace labarai.

Tabbas, babu wata matsala idan saboda fito da gaskiya an binciki manyan gidajen jarida kamar BBC, don fayyace matsayar da suke alfahari da ita cewa su 'tushe ne mai 'yanci na samun labarai ba tare da suna son-kai ba'.

#