Osimhen, wanda yanzu shi ne zakaran kwallon kafar Italiya, ya doke dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah da dan wasan Paris Saint-Germain da Maroko Achraf Hakimi inda ya lashe kyautar.

CAF 2023: 'Yan Nijeriya Victor Osimhen da Asisat Oshoala sun lashe kyautar gwarazan 'yan kwallon Afirka

'Yan Nijeriya Victor Osimhen da Asisat Oshoala sun lashe kyautar gwarazan 'yan kwallon Afirka na CAF 2023 a rukunin maza da mata a bikin da aka gudanar a Marrakech, babban birnin Maroko ranar Litinin da maraice.

Osimhen, wanda yanzu shi ne zakaran kwallon kafar Italiya, ya doke dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah da dan wasan Paris Saint-Germain da Maroko Achraf Hakimi inda ya lashe kyautar.

Oshoala, mai shekara 29, tana cikn 'yan wasan Nijeriya mata da suka kai zagayen 'yan-goma-sha-shida a Gasar Kwallon Kafa ta FIFA da aka gudanar a bazara a kasashen Australia da New Zealand ko da yake Ingila ta fitar da su daga gasar.

#