An yi baje-kolin ne domin jan hankulan duniya game da bala'i da mawuyacin halin da yaran Falasdinu ke ciki sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai musu.
Daraktan Sadarwa ya jan hankalin duniya game da mawuyacin halin da yaran Gaza ke ciki a yayin bude baje-kolin zane-zane da aka yi a kansu.
An bude baje-kolin mai suna "Bulletproof Dreams: Gaza Child Artists Exhibition" a Turancin Inlgilishi a Dandalin Taksim da ke birnin Istanbul ranar Juma'a wanda ya samu halartar Mai Dakin Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan da Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun.
"Dole mu zama muryar kananan yara Falasdinawa wadanda (Isra'ila) ta kwace 'yancinsu na rayuwa," in ji mai dakin shugaban kasa, tana mai jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da kokarin da take yi na kawo karshen cin zarafin da Isra'ila take yi wa Falasdinawa.
Shi ma Altun ya yi makamancin wannan jawabi a yayin da ya sha alwashin cewa Turkiyya ba za ta taba karaya ba wajen fadin gaskiya, kuma ba za ta taba daina kare hakkin kananan yara da ake kashewa ba.
"Muguntar Isra'ila ba ta da hallacci kowanne iri...Wannan ya nuna cewa babu shakka Isra'ila tana nufar kananan yara ne da makomar Falasdinu a yakin da take yi, inda take aikata laifukan yaki da kuma yin kisan kare-dangi," a cewar daraktan sadarwar.
Nuna yaki da barna
Dan jarida Abdullah Aytekin ne ya tattara zane-zanen da aka yi baje-kolinsu, wadanda suka kai guda 266, da yaran Gaza, ciki har da wadanda Isra'ila ta kashe, suka yi.
Mona, 'yar shekara 6 daga Gaza wadda ta ga lokacin da Isra'ila ta kashe mahaifiyarta a Yakin Gaza na 2008-09 da kuma kisan 'yan uwanta 26, na cikin wadanda suka yi zane-zanen.
Zane-zanen, "Bulletproof Dreams: Gaza Child Artists Exhibition", mai fadin sikwaya mita1350, an yi su ne domin jan hankalin duniya game da bala'in da yaran Gaza ke ciki sakamakon hare-haren Isra'ila.
Kazalika akwai bangaren da aka yi baje-kolin zane-zane na 'yan jarida da likitoci da suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kaddamar tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan Hamas ta kai mata harin ba-zata.
Tun daga wancan lokacin, Isra'ila ta kashe Falasdiawa akalla 21,110, galibinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata 55,243, a cewar hukumomi.