An yi amannar cewar helikwafta samfurin Bell 212 da ya yi hatsari a arewacin Iran lamarin da ya yi sanadin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da tawagarsa, ya kai aƙalla shekara 45 da ƙerawa kuma bayanai sun ce rundunar sojin Iran tana da irinsa guda 10.

Bayani kan jirgin helikwafta ƙirar Amurka da ya yi hatsari da shugaban Iran Raisi

Amurka ce ta ƙera jirgin helikwafta samfurin Bell 212 wanda ya yi hatsari a birnin Tabriz na arewacin Iran ranar Lahadi lamarin da ya yi sanadin mutuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa waɗanda suka taso daga Azerbaijan.

Babu fasinjan da aka gano da ransa lokacin da aka gano tarkacen jirgin, wanda Iran ta saya daga Amurka shekaru da dama da suka wuce kafin juyin-juya-halin ƙasar na 1979.

An soma ƙera jirgin samfurin Bell 212 a garin Fort Worth na jihar Texas, kafin a sauyawa kamfanin matsuguni zuwa birnin Mirabel da ke yankin Quebec na ƙasar Canada a 1988, sannan ya daina aiki a 1998.

Ko da yake sojoji sun soma aiki da jirgin ne a 1968, an fi amfani da shi a matsayin jirgin fasinja.

Jirgin samfurin Bell 212 yana iya ɗaukar fasinja 15, ciki har da ma'aikatan cikin jirgin.

Ana iya amfani da shi wurin yaƙi da ɗaukar kaya da sauransu.

Bayanai sun ce an inganta helikwaftan da Raisi ya hau don ya iya ɗaukar fasinja 15.

Na'urorin jirgin

Jirgin samfurin Bell 212, wanda direba ɗaya ko biyu za su iya tuƙawa, yana da tsayin mita 17.41, sannan yana da tsawon mita 3.83 daga ƙasa zuwa sama.

Yana da nauyin kiligiram 2,962 idan ba ya ɗauke da kaya, kuma yana iya ɗaukar kaya masu nauyin da ya kai kiligiram 5,080, kana injinsa yana da nauyin kilowat 1,300 da farfela guda biyu, kowace tana da tsawon mita 14.63.

Jirgin yana iya gudun da ya kai kilomita 190 duk awa ɗaya amma zai iya kai wa kilomita 220 idan zai yi yaƙi.

Kazalika yana iya tafiya mai nisan kilomita 439 sannan ya kai ƙololuwar nisan da ya kai ƙafa 17,388.

#