Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan.

Bayanai kai-tsaye kan rikicin Iran da Isra'ila: Iran ta musanta iƙirarin kai mata harin 'makamai masu linzami', ta ce ta lalata jirage 3 maras matuƙa na Isra'ila

0050 GMT — Iran ta musanta iƙirarin kai mata harin 'makamai masu linzami', ta ce ta lalata jirage 3 maras matuƙa na Isra'ila

Wani jami'in gwamnatin Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labaran a Reuters cewa babu wani harin makamai masu linzami da aka kai a cikin ƙasarsu, yana mai ƙaryata rahotannin kafafen watsa labaran Amurka da ke cewa Isra'ila ta kai musu hari.

An ambato kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran yana cewa ba a kai musu harin makamai masu linzami ba, inda ya ƙara da cewa na'urorinsu sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa da dama daga sararin samaniyar yankin Isfahan.

Sai dai jami'an gwamnatin Amurka biyu sun tabbatar wa CBS News cewa wani makami mai linzami na Isra'ila ya sauka a Iran. Reuters ya ruwaito cewa Isra'ila ta gaya wa Amurka shirinta na kai wa Iran hari.

Wasu jami'an gwamnatin Amurka da ba sa so a ambace su sun shaida wa CBS News cewa Isra'ila ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango a harin da ta kai wa Iran.

0040 GMT — Isra'ila ta kai a Iran harin makamai masu linzami

Isra'ila ta kai a Iran harin makamai masu linzami, in ji ABC News, wanda ya ambato jami'an gwamnatin Amurka.

Kazalika kamfanin dillancin labara na Fars news da ke Iran ya bayar da rahotanni fashewar wasu abubuwa a filin jirgin saman tsakiyar Isfahan, ko da yake ba a san dalilin aukuwar fashewar ba.

"Har yanzu ba a san dalilin akuwar fashewar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin wannan lamari," in ji Fars news agency. An soma juya akalar jiragen fasinja ranar Juma'a da safe a yammacin Iran, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

A ƙarshen makkon jiya, Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a Isra'ila don yin raddi kan harin da Isra'ila ta kai ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Syria.

A birnin Isfahan ne ake da manyan filayen jiragen saman sojin Iran, da kuma tashoshin nukiliyarta. Jami'an gwamnatin Iran ba su bayar da martani ba kawo yanzu. Isfahan na da nisan kilomita 350 daga Tehran, babban birnin Iran.

A birnin Isfahan ne ake da manyan filayen jiragen saman sojin Iran, da kuma tashoshin nukiliyarta. / Hoto: TRT World

2240 GMT — Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Iran jerin takunkumai kan harin da ta kai wa Isra'ila

Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Iran jerin takunkumai a fannin jirage marasa matuƙa na sojinta sakamakon harin da ta kai wa Isra'ila da makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a ƙarshen mako.

"A yau, za mu ɗauki mataki kan Iran — za mu sanya mata sabbin takunkumai da taƙaita abubuwan da za ta fitar ƙasashen waje," a cewar shugaban Amurka Joe Biden a wata sanarwa da ya fitar.

"Harin da gwamnatin Iran ta kai wa Isra'ila na ganganci ne kuma yana da hatsari na watsuwar rikici," in ji Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, inda ya ƙara da cewa Birtaniya ta sanya takunkumai kan "shugabannin sojoji da rundunonin tsaron Iran waɗanda suke da nauyin kai harin ƙarshen mako."

Iran ta ƙaddamar da hari kai-tsaye karon farko zuwa cikin Isra'ila ranar Asabar domin yin martani kan harin da Isra'ila ta kai a ofishin jakadancinta da ke Damascus ranar 1 ga watan Afrilu inda ta kashe zaratan sojojin runduna ta musamman ta Islamic Revolutionary Guard Corps, ciki har da janar guda biyu.

#