Aƙalla mutane biyar ne suka mutu, yayin da 22 suka jikkata sakamakon harin ta'addanci da aka kai Kamfanin Ƙera Jiragen Sama na Turkiyya (TAI).

Ƙasashen Afirka sun soki harin ta'addanci da aka kai a Turkiyya

Mali, Senegal, Somalia da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun yi Allah wadai da mummunan harin ta'addanci da aka kai a ranar Laraba a masana'antar kayan tsaro ta Turkiyya a babban birnin ƙasar.

"Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na suka da babbar murya d aharin 'yan ta'adda a Ankara. Zukatanmu na tare da 'yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma muna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar a wata sanarwa da ta fitar.

"JDK na sake jaddada goyon bayanta ga Turkiyya a matakin da ta dauka na yaki da dukkan nau'ikan ta'addanci," in ji

Tun da fari, shugaban gwamnatin wucin gadi ta Mali, Janar Assimi Goita ma ya la'anci harin.

"Muna suka da babbar murya ga harin 'yan ta'adda kan hwalkwatara Masana'antar Kayan Sufurin Jiragen Sama ta Turkiyya da ke Ankara," in ji Goita a wata sanarwa.

'Cikakken goyon baya'

Da yake bayyana "cikakken goyon baya" ga Turkiyya, ya ce "Babbar abokiyar Mali ta fuskar tsaro", kuma zukatansu na tare da 'yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su.

A kalla mutane biyar ne suka mutu, yayinda wasu 22 suka jikkata sakamakon harin ta'addanci kan Kamfanin Samar da Jiragen Sama na Turkiyya (TAI).

Yerlikaya ya kara da cewa an kashe maharan.

Shugaban Kasar Sanagal Bassirou Diomaye Faye ya bayyana harin a matsayin 'na matsorata'.

"Ina la'antar harin 'yan ta'adda a Turkiyya. Hari ne mummuna na matsorata. A madadin jama'ar Sanagal, ina bayyana kauna da goyon bayanmu ga Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da dukkan jama'ar Turkiyya," in ji Faye.

"Ina fatan samun aminci ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."

'Aika-Aikar matsorata'

Somalia ma ta la'anci harin, inda ta kira shi da "mummunan" harin ta'addanci.

"Wannan harin na matsorata ba Turkiyya kawai aka kai wa ba, barazanar tsaro ce ga dukkan duniya. Saboda yadda Somalia ke fuskantar irin wannan kalubale, tana jajantawa Turkiyya," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Somalia ta fitar.

Somalia ta kuma yaba da mataki nan da nan da jam'ian tsaro suka dauka, kuma sun yi amannar za a zartar da hukunci ga wadanda suka yi aika-aikar.

Mogadishu na mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda ibtila'in ya shafa, kuma kasar na tare da jama'a da gwmanatin Turkiyya.

"Somalia na tare da Turkiyya da sauran kasashen duniya kan batun yaki da ta'addanci, tare da hadin kai mai tushe a al'adun bai daya da aminta da juna," in ji sanarwar da aka fitar, tana mai kira ga kasashen duniya da su "karfafa hadin kai wajen yaki da ta'addanci."

"Tare za mu iya tabbatar da irin wadanan aika-aika ba su raunata yunkurinmu na kare jama'armu da wanzar da zaman lafiya ba," in ji sanarwar.

#