Sakamakon zaɓen ya yi babbar illa ga Shugaba Emmanuel Macron, tare da jefa ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a yankin Turai cikin rashin tabbas.

Ana fargabar jirkicewar manufofin ƙasa a Faransa sakamakon sauyin siyasa

Faransa na fuskantar rikicewar majalisar dokoki kuma a ranar Litinin din nan za a fara tattaunawar ƙulla yarjejeniyar kafa gwamnati, bayan da jam'iyyar masu sauƙin ra'ayi ta bayar da mamakin yin nasara tare da hana jam'iyyar Marine Le Pen mai tsaurin ra'ayi kafa gwamnati.

Jam'iyyar NFP ta masu sauƙin ra'ayi ta zama wadda ta fi kowacce yawan kujeru a majalisar dokokin Faransa bayan zaɓen na ranar Lahadi, amma babu wata jam'iyya da ta samu adadin kujerun da zai ba ta ikon kafa gwamnati ita kaɗai, sai dai ko a yi ƙawance a kafa gwamnati ko a kafa gwamnati mara rinjaye.

Sakamakon zaɓen ya yi babbar illa ga Shugaba Emmanuel Macron, tare da jefa ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a yankin Turai cikin rashin tabbas na siyasa, a lokacin da ya rage makonni Paris ya karɓi baƙuncin gasar Wasannin Olympics.

Sakamakon zaɓen majalisar dokokin na iya yin illa ga rawar da Faransa ke takawa a Tarayyar Turai, kuma hakan zai sanya da wahala wata jam'iyyar ta iya fitar da wata manufa a cikin gida.

Firaminista ya yi murabus

Babu tabbas kan yadda manufofin Faransa za su kasance a Afirka, inda take fuskantar suka da koma baya a 'yan shekarun nan saboda abinda da yawan mutane ke wa kallon na zuwa ne saboda yadda take ci gaba da tsoma baki a al'amuran cikin gida na kasashen nahiyar tare da kwashe albarkatun kasa da arzikinsu.

Jam'iyyar masu saukin ra'yi ta lashe kujeru 182, am'iyyar Macron ta lashe 168 da NR ta Marine Le pen ta lashe kujeru 143, kamar yadda jaridar Le Monde ta bayyana alkaluman ma'aikatar harkokin cikin gida.

Firaminista Gabriel Attal ya ce zai mika takardar yin murabus, amma ba a tabatar ko shugaban kasa zai amince da murabus din nan take ba, saboda nauyin da ake da shi na kafa sabuwar gwamnati. Attai ya ce zai iya zama a matsayin na riko.

"Tabbas zan sauke nauyin da ke kaina matukar an bukaci hakan - ba za a ga sabanin hakan ba a wannan lokaci d aake gaf da karbar bakuncin Gasar Olympics da ke da muhimmanci ga kasarmu," in ji Attal, a lokacinda kawance karkashin Macron ya tashi a tutar babu.

'Gibin Ayyukan Majalisar Dokoki'

Jama'ar bangaren NFP - sun fito ne daga jam'iyyar Kwaminisanci ta Faransa, jam'iyyar masu sassaukan ra'ayi, Jam'yyun Green da Socialist - sun kuma gana kan yadda za su ci gaba da tafiya tare.

Jean-Luc Melenchon madugun 'yan adawa a Faransa ya ce lallai Firaministan zai fito ne daga kawancen NFP. Sai dai kuma, kawnace ba shi da shugaba, kuma kawunan jam'yyun a rarrabe yake kan waye za su zama a matsayin Firaminista.

Wasu sanannun masu matsakaicin ra'ayi da suka hada da Edouard Philippe, tsohon firaminista a karkashin gwamnatin Macron, na cewa a shirye suke ru yi iki don tabbatar da samar da gwamnati tsayayyiya.

Euro ya fadi a ranar Lahadi bayan an sanar da sakamakon zaben.

"Tabbas za a samu gibi babba idan aka zo maganar ayyukan majalisar dokokin Faransa," in ji Simon Harvey, shugaban sashen nazari na FX da Monex Europe a Landan.

'Kawance mai ban kunya'

Ga jam'iyyar RN ta Le Pe, sakamakon zaben ya nesanta da abinda suka gani makonni kadan kafin zabe a yayin jin ra'ayin jama'a, wand ake nuni da a su lashe zabe ba tare da wata matsala ba.

Masu sauki da matsakaicin ra'ayi sun hada kai waje guda bayan zagayen farko na zaben makon da ya gabata inda suka samu adadin da ya kalubalanci RN a zabaye na biyu.

A mayar da martani na karon farko, shugabar RN Jordan Bardella kuma yarinyar Le Pen ta kira kawancen masu kalubalantar RN da "kawance mai ban kunya" inda ta ce hakan zai raunata Faransa.

Akwai yiwuwar Le Pen ce za ta tsaya wa jam'iyyar takarar shugaban kasa a zaben 2027, inda take cewar ganin yadda a wannan karon jam'iyyar ta smau kuri'u sama da zabukan shekarun baya, alamu ne da ke haskaka samun makoma mai kyau a nan gaba.

Ta ce "An jinkirta samun nasararmu ne kawai."

Toshe damar masu ra'ayin rikau

A yayin da aka fada duhu a ranar Lahadi, masu goyon bayan jam'iyyar mai saukin ra'ayi sun haskaka mutum-mutumin 'Marianne' a 'Place de la Republique' yayin murnar lashe zabe. Marianne wata alama ce ta kasa ta Faransa da ke nufin dalili, 'yanci da manufofin jumhuriya.

Baptiste Fourastie, mai zane dan shekara 23 da ke Place de la Republique ya bayyana cewa "Ba mu tsammaci haka ba, haka ma sakamakon zaben. Muna urnar yadda jama'ar Faransa suka yi nasara karo na biyu ta hanyar toshe damar masu ra'ayin rikau."

Sai dai kuma, ya bayyana damuwar cewa akwai yiwuwar masu ra'ayin rikau su kara samun karbuwa tare da lashe zabe a nan gaba matukar gwamnati mai zuwa ba ta yi abinda ya kamata ba.

Ya ce "Zai yi wahala da majalisar dokoki da ta warwartsu tsakanin jam'yyu, amma hakan ya fi da a ce tana karkashin masu ra'ayin rikau."

#