"Da tashoshimu  irin su TRT World da kuma TRT Arabic, tare da sashin labaranmu na dijital na duniya, mun bunkasa zuwa wata cibiyar watsa labarai da ke shaida wa duniya abin da ke faruwa a duniya," in ji Mehmet Zahid Sobaci.

An zabi Darakta Janar na TRT Sobaci a matsayin shugaban babbar kungiyar watsa labarai ta duniya

An zabi Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci a matsayin shugaban kungiyar Asia-Pacific Broadcasting Union (ABU) yayin taronta karo na 60.

"Zaben da aka yi mini a matsayin shugaban ABU yana da muhimmanci da manufar Turkiyya ta jagora a kowanne fanni a duniya,” in ji Sobaci, inda ya kara da cewa shugabancin ABU yana da matukar muhimmanci domin kuwa ya zo a daidai lokacin da kasar ta cika shekara 100 da zama Jamhuriya.

Taron ABU, wadda ita ce kungiyar kafafen watsa labara mafi girma a duniya inda fiye da mutum biliyan 3.5 suke kallon kafafen watsa labaran da ke karkashinta kuma take da mambobi 246 daga kasashe 65, an yi shi ne a birnin Seoul daga 31 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, 2023 karkashin jagorancin Hukumar watsa labarai ta South Korean Broadcasting System.

“Turkiyya tana ci gaba da daukaka da kuma kuma karfi a matsayinta na jagora. Jamhuriyar Turkiyya ta hada kowanne fanni, ciki har da siyasar cikin gida da manufofin kasashen waje da fannin makamashi, muhalli, masana'antu, ilimi da fasaha,” in ji Sobaci.

“Wannan lokaci ne nuna burin Turkiyya, da kuma kwazonta na cim ma abubuwan da ta sanya a gaba. Don haka, muna kallon shugabancin ABU a matsayin wani mataki na taimakawa wajen cim ma muradun Turkiyya a fannin harkokin watsa labarai na duniya," a cewarsa.

'TRT tana shaidu wa duniya abin ke faruwa a duniya'

Sabon zababben shugaban ABU kuma Darakta Janar na TRT ya jaddada mahimmancin tashoshin da kafar watsa labarai nTurkiyya TRT da ke karkashin gwamnatin kasar.

"Da tashoshimu irin su TRT World da TRT Arabic, da kuma sashin labaranmu na dijital na duniya, mun bunkasa zuwa wata cibiyar watsa labarai da ke shaida wa abin da ke faruwa a duniya," in ji Sobaci.

“Yayin da muke ci gaba da wannan aiki, ba mu yi watsi da nauyin da ke wuyanmu ba. Mun himmatu wajen gabatar da batutuwan da suka shafi ci gaba da rikice-rikice da ke faruwa a duniya ta fuskar daidaiton adalci,” in ji shi.

#