Zaman ɗarɗar da ke ƙaruwa na zuwa ne a lokacin da aka sake sabunta arangama tsakanin dakaru masu biyayya ga abokan hamayyar biyu a garin Nasir da ke Jihar Upper Nile mai arzikin man fetur.
An tsare matamakin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu na farko Riek Machar, wanda ya daɗe a matsayin abokin hamayyar Shugaba Salva Kiir, a gida, in ji jam’iyyarsa.
Wani jerin gwanon jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin manyan jami’an tsaro ciki har da ministan tsaro ya shiga gidansa a babban birnin ƙasar, Juba, kuma ya ƙwace ɗamar yaƙin dogaransa ranar Laraba da maraice, in ji jam’iyyar SPLM/IO.
"A iya cewa, Dr Machar yana a tsare a gidansa, amma jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin ɗauke shi daga farko," in ji Reath Muoch Tang, shugaban kwamitin harkokin wajen jam’iyyar.
Kawo yanzu dai gwamnatin ƙasar ba ta yi tsokaci kan lamarin ba.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwan biyu tana gargaɗi cewa Sudan ta Kudu na daf da komawa yaƙin basasa bayan rashin jituwa tsakanin Machar da shugaban ƙasar ya ƙara tsanani, lamarin da ya shafe makonnin yana tsananta.
Shugabannin biyu sun cim ma yarjejeniya a watan Agutsan shekarar 2018, yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen yaƙin basasa na shekara biyar wanda ya kashe kusan mutum 400,000.
Amma cikin shekaru bakwai da suka wuce dangantakar tsakaninsu tana ƙara tsami cikin tashin hankalin ƙabilanci da kuma arangama da ake lokaci-lokaci.
Jam’iyyar SPLM/IO ta ce an tsare Machar tare da matarsa Angelina Teny, wadda ita ce ministar cikin gidan ƙasar.
"An ba shi sammacin kamu kan wasu zarge-zargen da ba bayyana ƙarara ba," in ji Tang a wata sanarwa, yana mai bayyana matakin a matsayin "ƙeta kundin tsarin mulki da yarjejeniyar zaman lafiya da gangan ".
"Tsare mataimakin shugaban ƙasa na farkon ba tare da bin ƙa’ida ba na yi wa tsarin bin doka zagon ƙasa tare da yi wa kwanciyar hankalin ƙasar barazana," in ji shi.
Ofihsin MDD a Sudan ta Kudu ya yi gargaɗin cewa ƙasar da ta fi ƙarancin shekaru a duniya na fuskantar barazanar rasa "nasarorin da aka samu da wahala cikin shekaryu bakwai da suka wuce " idan ta koma "matakin yaƙi ", bayan rahotannin tsare Machar sun bayyana.
"A wannan daren, shugabannin ƙasar suna daf da komawa yaƙe-yaƙe mai yawa," kamar yadda ofishin ya faɗa a wata sanarwa ranar Laraba.
Saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiyar shekarar 2018 "ba wai ɓarna kawai zai yi wa Sudan ta Kudu ba, amma kuma zai kuma shafi yankin gabaɗaya," in ji ofishin.
Ofisoshin jakadancin Birtaniya da Amurka sun rage yawan jami’an diflomasiyyarsu tare da shawartan ‘yan ƙasashensu su bar ƙasar yayin da aka rufe ofisoshin jakadancin ƙasar Norway da Jamus a Juba.
Zaman ɗar-ɗar da ke ƙaruwa na zuwa ne a lokacin da aka sake sabunta arangama tsakanin dakaru masu biyayya ga abokan hamayyan biyu a garin Nasir da ke jihar Upper Nile State mai arziƙin man fetur.