Jirgin SpaceX Dragon Capsule Freedom mai ɗauke da ma'aikatan Axiom Mission 3 (Ax-3), ciki har da ɗan sama jannatin Turkiyya na farko Alper Gezeravci, ya dawo duniya cikin nasara.

Ɗan sama jannatin Turkiyya na farko ya dawo duniya daga tafiyar da ya yi zuwa sararin samaniya

Jirgin SpaceX Dragon Capsule Freedom mai ɗauke da ma'aikatan Axiom Mission 3 (Ax-3), ciki har da ɗan sama jannatin Turkiyya na farko Alper Gezeravci, ya dawo duniya cikin nasara inda ya sauka a Gaɓar Tekun Florida, bayan zamansu na kwanaki 18 a tashar sararin samaniya ta kasa da kasa (ISS).

Kumbon ya bar jikin tashar ISS a ranar Laraba kuma ya fara bulaguron komawa duniya.

Tsarin dawowar ya ɗauki kusan awa 47 inda tafiyar ta kawo ƙarshe a ranar Juma'a, lokacin da jirgin ya gangara kan teku. Tawagar da ke jiran isarsa ta kwaso matafiyan cikin gaggawa daga cikinsa.

Tawagar da ke cikin jirgin na Ax-3 na Turai sun haɗa da babban ɗan sama jannati na Axiom Space da tsohon kwamandan ISS Michael Lopez-Alegria, wanda ke wakiltar Spain da Amurka a matsayin kwamandan tawagar Ax-3. A shekarar 2022, ya jagoranci Axiom Mission 1 (Ax-1), a tafiya ta farko ta ƙashin kai da ISS.

Matukin jirgin shi ne Kanar Walter Villadei daga Rundunar Sojan Sama ta Italiya. Gezeravci, matukin jirgin saman F-16, yana shiga cikin Ax-3 a matsayin ƙwararre a harkar, tare da ɗan sama jannatin Sweden Marcus Wandt daga Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai.

An harba jirgin Ax-3 ne daga cibiyar binciken sararin samaniya ta NASA ta Kennedy da ke Florida a ranar 19 ga watan Janairu, a kan wata roka kirar SpaceX Falcon 9.

Tawagar da ke cikinsa sun tsaya a tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa a washegarin ranar 20 ga Janairu.

A tsawon sama da mako biyu da suka yi a tashar, matukin jirgin saman Turkiyya Kanar Alper Gezeravci tare da ma'aikatansa uku daga Spain da Italiya da Sweden sun gudanar da gwaje-gwajen kimiyya sama da 30, kusan rabinsu na Gezeravci da kansa.

An dage dawowar ma'aikatan jirgin sau da yawa saboda rashin kyawun yanayi.

#