Sabon zababben shugaban kasar zai fuskanci matsin lamba don cika alkawururrukan zabe cikin sauri a lokacin da ba a amincewa da tsarin siyasar Gana.

An rantsar da sabon Shugaban Kasar Ghana John Mahama

An rantsar da John Dramani Mahama a matsayin Shugaban Kasar Ghana a ranar Talata inda zai tunkari kalubalen da aka san kasar na fama da su, ciki har da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da hauhawar farashi da rashin walwalar jama'a.

Madugun 'yan adawar mai shekaru 66, ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 7 ga Disamba da babban rinjaye inda ya sake dawowa shugabancin kasar ta Yammacin Afirka, ta biyu mafi girma wajen samar da cocoa a duniya.

Mahama ya maye gurbin Nana Akufo-Addo, wanda ya sauka bayan kammala wa'adi biyu na shugabanci, bisa dorewar dimokuradiyyar Gana a yankin da a baya ya sha fama da juyin mulkin soja da hare-haren ta'addanci.

A yayin rantsar da shi a Accra, Mahama ya yi alkawarin "sauya fasalin'" Ghana tare da habaka tattalin arzikin kasar.

Ya kuma gode wa 'yan kasar ta Gana saboda zabar sa da suka yi a zaben na watan Disamba.

"Akwai fata mai kyau. Yau rana ce ta farkon sabuwar dama, dama da muke da ita ta kawo suyi a shugabanci da kula da tattalin arziki.

"Dole ne mu sake suaya fasalin kasarmu Gana da muke kauna," Mahama ya yi alkawari.

Bayan annobar COVID-19, rikicin tsadar rayuwa, kokarin kubuta daga basussukan IMF da na wasu kasashen, sun durkusa da tattalin arzikin Ghana wanda a yanzu ke farfadowa.

#