Kakakin Rundunar 'yan sandan jihar Kano Abdullahi Kiyawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa an kama mutumin da ake zargi da cinna wa masallacin wuta sannan ya rufe ƙofa, abin da ya sa mutane da dama suka jikkata.

An kona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a garin Larabar Abasawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da TRT Afrika Hausa faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

"Na yi magana da wanda ake zargi da aikata laifin, zan yi muku ƙarin bayani bayan kammala tattara bayanai," a cewar Abdullahi Kiyawa.

Rahoatanni sun ce an garzaya da mutanen da suka jikkata sakamakon faruwar lamarin asibiti, inda suke karɓar magani, sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani kan ko an samu asarar rayuka.

Za mu kawo ƙarin bayani nan gaba

#