Sojojin waɗanda daga ciki akwai biyu masu muƙamin manjo da kyaftin ɗaya sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki lokacin da ake wani rikicin ƙabilanci.

An kashe sojojin Nijeriya 15 a Jihar Delta

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta tabbatar da mutuwar wasu sojojinta 15 a Jihar Delta.

Daraktan watsa labarai na sojin ƙasar Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya tabbatar da mutuwar sojojin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce sojojin sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki lokacin da ake wani rikicin ƙabilanci a Ƙaramar Hukumar Bomadi ta Jihar Delta.

Rundunar tsaron Nijeriyar ta tabbatar da cewa an kashe masu muƙamin manjo biyu sai kyaftin ɗaya sai sojoji 12.

Rahotanni daga jihar sun ce sun rasu a lokacin da suka yi ƙokarin kwantar da wata tarzoma wadda ta ɓarke tsakanin yan ƙabilar Okuama da Okoloba a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Shugaban Sojojin Nijeriya Christopher Musa ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar sojojin.

Janar Tukur Gusau ya bayyana cewa tuni aka soma bincike haka kuma an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargin suna da hannu a kisan sojojin.

#