Mutanen da ke hanyar zuwa masallaci domin gudanar da sallar Asubah sun juya sun koma gidajensu saboda ƙarar bindigar.
An ji karar harbe-harbe da sanyin safiyar Talata a wasu yankuna na Bamako babban birnin kasar Mali, kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
An ji ƙarar harbe-harben bindigar a unguwar Banankabougou.
Mutanen da ke hanyar zuwa masallaci domin gudanar da sallar Asubah sun juya sun koma gidajensu sakamakon ƙarar bindigar.
Mutanen sun bayyana cewa harbin bindigar ya fara ne da misalin ƙarfe 5:30 na Asuba.
Wasu sun ce harbin ya fito ne daga ɓangaren filin jirgi, wasu kuma sun ce daga ɓangaren ‘yan jandarma ne.
Wata majiya ta tsaro ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran cewa an ji harbin bindigar a unguwanni daban-daban na Bamako, ciki har da waɗanda ke kusa da filin jirgi.
Kasar Mali dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da dama da ke yaki da ‘yan tawaye masu iƙirarin jihadi da suka adabbi arewacin ƙasar tun daga shekara ta 2012, kuma tun daga nan suka bazu a yankin Sahel da kuma a baya-bayan nan zuwa arewacin kasashen da ke gabar teku.
Dubban mutane ne aka kashe tare da raba miliyoyi da muhallansu a yankin a daidai lokacin da sojojin ƙasar ke ƙoƙarin yaƙar 'yan ta'addan, inda ake zargin gwamnatoci da mayaka da cin zarafin fararen hula.
Bacin rai ga hukumomi na kasa maido da tsaro ya taimaka wajen juyin mulki sau biyu a Mali - a 2020 da 2021 - biyu na makwabciyarta Burkina Faso da daya a Nijar.
Bacin rai na rasa kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar ya jawo juyin mulki sau biyu a Mali - a 2020 da 2021 – inda maƙwabtan ƙasar biyu su ma suka biyo baya da juyin mulki wato Nijar da Burkina Faso.