Tun da safe masu zaɓe suka soma jefa ƙuri'a a rumfunan zaɓe a faɗin jihar, inda ma'aikatan Hisbah da Karota suka bayar da tsaro a rumfunan zaɓen sakamakon ƙaurace wa zaɓen da 'yan sanda suka yi.
A ranar Asabar aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Kano.
Rahotanni daga jihar na cewa tun da safe masu kaɗa ƙuri’a suka fita zaɓe a jihar domin zaɓen kansiloli da kuma shugabannin ƙananan hukumomi.
Jam’iyyu shida ne ke suka fafata a zaɓen ƙananan hukumomin, kamar yadda shugaban hukumar zaɓen ta Kano Sani Malumfashi ya tabbatar.
Jam’iyyun sun haɗa da Nigeria People Party (NNPP), Zenith Labour Party (ZLP) Accord Party (AP) National Rescue Movement (NRM), African Action Congress (AAC) and Action Alliance (AA).
Jam’iyyar APC ta sanar da ƙaurace wa wannan zaɓen. Sai dai wannan zaɓen yana zagaye da tirka-tirka iri daban-daban domin tuni Kotun Tarayyar Nijeriyar ta haramta gudanar da wannan zaɓen inda ta ce akwai wasu mambobin hukumar zaɓen ta Kano KANSIEC waɗanda cikakkun ‘yan Jam’iyyar NNPP mai mulki ne a jihar.
Sai dai kotun jihar Kano ta yi hukunci wanda ya ci karo da na tarayya inda ita kuma ta umarci hukumar zaɓen ta Kano da ta gudanar da zaɓen a ranar Asabar.
Sai dai duk da wannan hukuncin na kotun, gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf ya ce babu gudu ba ja da baya wurin gudanar da wannan zaɓen.
Ita ma rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce za ta bi umarnin kotu, inda ta ce za ta ƙaurace wa zaɓen.
Rahotanni daga Kanon na cewa jami’an Hisbah da ‘yan Karota ne ke bayar da tsaro a rumfunan zaɓen da safiyar ta Asabar.