Wannan shafin ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

An aika da rukunin kayan agaji 'mafi girma' cikin Gaza tun bayan soma yaki

1517 GMT — Masar ta ce akwai yiwuwar Isra'ila da Falasdinu su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Kasar Masar a ranar Asabar ta bayyana cewa ta samu bayanai masu dadi daga duka bangarori kan yiwuwar tsaiwata yarjejeniyar tsagaita wuta da kwana daya ko biyu.

Diaa Rashwan wanda shi ne shugaban watsa labarai na gwamnatin Masar ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce kasar na gudanar da tattaunawa da duka bangarorin domin ganin an kara tsawaita yarjejeniyar ta kwanaki hudu.

Tuni aka soma shiga da kayayyakin abinci cikin Gaza sakamakon wannan yarjejeniyar. / Hoto:Reuters

Hakan na nufin “za a kara sakin karin mutanen da ake tsare da su a Gaza da kuma fursunonin Falasdinu a Isra’ila.” in ji sanarwar.

1410 GMT — An aika da rukunin kayan agaji 'mafi girma' cikin Gaza tun bayan soma yaki

Kungiyar Red Crescent Society ta Falasdinu ta tabbatar da cewa ta kai ayarin motoci 61 dauke da kayayyakin agaji zuwa cikin Gaza da arewacin Gaza, inda ta ce wadannan ne kayayyakin agaji mafi yawa da aka kai tun bayan soma yakin a ranar 7 ga watan Oktoba.

Gaza ta kasu kashi biyar: Arewacin Gaza da Birnin Gaza da Deir el-Balah da Khan Younis da Rafah.

1340 GMT Za a saki 'yan Isra'ila 14 da Falasdinawa 42 a rana ta biyu ta yarjejeniyar musayar fursunoni

Kasashen duniya da dama sun yi maraba da wannan yarjejeniyar ta tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Gaza. / Hoto:Reuters

Hukumomi a Isra'ila sun ce za a saki fursunonin yaki 14 'yan Isra'ila da ake rike da su a Gaza da kuma Falasdinawa 42 da ke Isra'ila bayan harin da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoba.

Za a saki fursunonin ne a rana ta biyu ta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila.

Hukumomin Fursuna sun tabbatar da cewa Falasdinawa 42 - duka maza da mata - za a sake su karkashin yarjejeniyar da aka yi wadda ta amince da yin musanyar Falasdinawa uku da dan Isra'ila daya, kuma wata majiyar gwamnatin Isra'ila ta ce za a mika mutanen 14 da aka yi garkuwa da su.

#