Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce bai kamata Amurka ta daina toshe duk wani ƙudiri na tsagaita wuta na Majalisar Dinkin Duniya ba, inda ya kara da cewa sauran kasashen Yammacin Duniya ma na da hannu wajen kai hare-haren Isra'ila.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya caccaki Amurka kan toshe ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta a Gaza, wanda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta kasa tun bayan barkewar rikici a ranar 7 ga Oktoba.
A ranar Alhamis Hakan Fidan ya ce "Amurka ce kadai ta ƙi yin wani abu don dakatar da kisan kiyashi da tsagaita wuta a Gaza."
Ya kara da cewa, "Bai kamata ta kara toshe duk wani ƙuduri na tsagaita wuta na MDD ba," yayin da yake magana kan matakin da Amurka ta dauka na ƙin kaɗa ƙuri'a kan ƙudurori biyu na MDD da ya jawo mata suka sosai, a cikin watan Oktoba da farkon wannan wata.
Babban jami'in diflomasiyyar ya kuma soki sauran kasashen Yammacin Duniya da cewa suna da hannu a hare-haren Isra'ila.
"Hanyar yadda Ƙasashen Yammacin Duniya da suke alfahari da ɗabi'unsu, ke da hannu a kisan gillar da ake yi a Gaza yana nuni da rugujewar tsarin duniya na yanzu," in ji shi.
Sai dai Fidan ya ƙara da cewa lamarin yana juyawa kuma "dan'adam na dawowa hayyacinsa" a Gaza.
"Mun ga kasashe da yawa, wadanda a da suka ƙaurace wa ko kuma (sun kada kuri'a) kan (kudirin tsagaita wuta), yanzu sun yanke shawarar tsayawa tare da Falasdinu," in ji shi.
Samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kai a matsayin mafita
Fidan ya kara da cewa "muna ganin an samu ci gaba a sannu-sannu" kan batun Gaza.
"Musamman Ƙasashen Yammacin Duniya da da farko suka yi shiru game da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi, yanzu ko dai sun kaɗa ƙuri'ar amincewa ko kuma sun ƙaurace wa kaɗa ƙuri'ar hukumar.
"A haƙiƙanin gaskiya wannan babbar nasara ce ba ga Falasdinawa kaɗai ba har ma da bil'adama," in ji Ministan Harkokin Wajen kasar.
Fidan ya kuma bayyana cewa, Turkiyya na magana kan Gaza, kuma a madadin dukkan bil'adama, Fidan ta ce, "Domin a daina kisan kiyashi cikin gaggawa, a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, a ba da damar agajin jinƙai, da kuma dakile wannan bala'i daga a lokuta da dama, ya kamata mu shiga cikin kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu."
Ya ƙara da cewa "Muna jaddada saƙonninmu kan wannan batu a fili kuma a kai a kai ga dukkan masu shiga tsakani."
Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai ta sama da ta kasa, ta kuma ƙaƙaba wa Gaza hari, tare da kai farmaki ta ƙasa, sakamakon harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Aƙalla Falasdinawa 18,608 ne aka kashe yayin da sama da 50,000 suka jikkata a harin da Isra’ila ta kai tun daga wancan lokacin, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.
Adadin wadanda suka mutu a hukumance na Isra'ila a harin Hamas ya kai 1,200, yayin da kusan mutane 139 da aka yi garkuwa da su ke hannunsu, a cewar alkaluman hukuma.