Rushewar gine-gine ya zama ruwan dare gama gari a Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, lamarin da ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci.

Ɗalibai 16 ne suka rasu sakamakon rushewar ginin makarantarsu a Jos na Nijeriya

Akalla dalibai 16 ne suka mutu a ranar Juma’a bayan da ginin wata makaranta da ke tsakiyar birnin Jos na jihar Filaton Nijeriya ta rufta a kan ɗaliban da suke rubuta jarabawa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce an jiyo ɗaliban da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai suna kukan neman agaji Makarantar ta Saint Academy da ke gundumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

Masu aikin ceto suna ta ƙoƙarin zaƙulo wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da iyaye ke neman ‘ya’yansu.

Ya zuwa yanzu dai jami'ai sun ce "dalibai da dama" sun mutu.

Wani ɗalibi Wulliya Ibrahim wanda ke asibiti a kwance saboda raunin da ya ji ya shaida wa AFP cewa: "Na shiga ajin bai fi minti biyar ba, sai na ji ƙarar, kuma abu na gaba shi ne na tsinci kaina a nan."

“Muna da yawa a ajin, muna rubuta jarabawar ne,” in ji shi.

A nata ɓangaren, hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce ginin bene mai hawa biyu na Saint Academy ya ruguje inda ya kashe “dalibai da dama” ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

"NEMA da sauran masu ruwa da tsaki a halin yanzu suna gudanar da bincike da ayyukan ceto," in ji ta.

Wani mazaunin wurin Chika Obioha ya shaida wa AFP cewa ya ga akalla gawarwaki takwas a wurin kuma wasu da dama sun jikkata.

"Kowa yana taimakawa don ganin ko za mu iya ceton mutane da yawa," in ji shi.

Ba a dai bayyana dalilin rugujewar ginin ba amma mazauna yankin sun ce ya biyo bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku da aka yi a Filato ne.

Rushewar gine-gine ya zama ruwan dare gama gari a Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, lamarin da ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci.

Akalla mutum 45 ne suka mutu a shekarar 2021 bayan da wani dogon bene da ake ginawa ya ruguje a gundumar Ikoyi da ke babban birnin tattalin arzikin Nijeriyar, Legas.

Sannan mutum 10 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani gini mai hawa uku a unguwar Ebute-Metta da ke Legas shekara guda bayan haka.

#