Ƙasar Côte d’Ivoire ta yi nasarar ɗaukar kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Nijeriya da ci 2-1 a wasan ƙarshe da suka fafata ranar Lahadi.

AFCON 2023: Côte d’Ivoire ta ɗauki kofin nahiyar Afirka

Ƙasar Côte d’Ivoire ta yi nasarar ɗaukar kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Nijeriya da ci 2-1 a wasan ƙarshe da suka fafata ranar Lahadi.

Tawagar Super Eagles ce ta soma cin ƙwallo ta hannun William Troost-Ekong gabanin a tafi hutun rabin lokaci inda ya doka ƙwallon da ka a ragar the Elephants.

Sai dai ɗan wasan Côte d’Ivoire Franck Kessie ya farke ƙwallon jim kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Muna ci gaba da sabunta wannan labarin...

#