Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 75 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 19,667, da jikkata wasu fiye da 52,586, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari.

Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya zarce 20,000

1652 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya zarce 20,000

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya ce akalla mutum 20,000 ne aka kashe a yankin Falasdinu tun bayan fara yaƙin.

Kimanin yara 8,000 da mata 6,200 na daga cikin wadanda hare-haren Isra'ila suka kashe, yayin da rikicin ke ci gaba da ruruwa sama da watanni biyu bayan ɓarkewarsa a ranar 7 ga watan Oktoba.

1440 GMT Rashin dakatar da hare-haren Isra'ila a Gaza abin kunya ne ga bil'adama: Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sake yin Allah wadai da gazawar Ƙasashen Yammacin Duniya wajen daƙile hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Zirin Gaza na Falasdinu, yana mai cewa abin kunya ne ga bil'adama.

"Tarihi zai hukunta waɗanda suka haddasa wannan mummunan yanayi, da wadanda suka yi ƙoƙarin halasta shi, da wadanda suka yi watsi da shi," in ji Erdogan, yayin da yake magana a wajen bikin karramawar al'adu da fasaha na shugaban kasa a Ankara ranar Laraba. .

Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa, "Abin kunya ne ga bil'adama kasancewar manyan ƙasashe da dama ba su da wani ƙarfi wajen tunkarar munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa da ya jawo kisan kiyashi da sata."

Bayan haka Erdogan ya bayyana fatansa cewa "2024 za ta kasance shekarar da azzalumai za su fuskanci hukuncin da ya dace da su, kuma za a warke raunukan waɗanda aka zalunta."

1413 GMT Kaso 90 cikin 100 na jama'ar Gaza sun rasa muhallansu — MDD

Hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza sun yi sanadin raba kashi 90 cikin 100 na mazauna yankin da muhallansu, kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

“An lalata kusan kaso 60 cikin 100 na ababen more rayuwa da ke Gaza,” kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu ta bayyana.

Daga cikin wadanda Isra'ila ke kashewa har da 'yan gudun hijira wadanda suka rasa muhallansu. / Hoto: Reuters

0827 GMT Isra'ila ta kashe gomman Falasdinawa a harin da ta kai da asubahi

Jirgin yakin Isra’ila da makaman atilare na kasar sun yi aman wuta a wurare da dama a Gaza, inda suka fi mayar da hankali kan Jabalia da kuma Khan Younis da ke arewaci da kuma tsakiyar yankin.

Harin da aka kai a Jabalia na zuwa ne bayan wani mummunan lamarin da ya faru a daren da ya gabata inda aka rasa farar hula 20 da kuma raunata sama da 70, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu wato WAFA ya ruwaito.

Majiyoyin kiwon lafiya sun kuma tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kashe iyalan gidan Anan sama da 13 daga ciki har da mata da yara.

0720 GMT — Isra'ila ta ce an kashe sojanta daya an raunata 15 cikin kwana guda a Gaza

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da mutuwar daya daga cikin sojojinta a yayin arangamar da dakarunta suke yi da mayakan Falasdinu a kudancin Gaza, wanda hakan ya sa adadin sojojin na Isra’ila da suka mutu ya kai 465 tun daga 7 ga watan Oktoba.

“Kyeftin Linor Sion (mai shekara 32), wanda sojan yaki ne a bataliya ta 363, an kashe shi a kudancin Zirin Gaza,” kamar yadda kafar watsa labaran Isra’ila ta sanar.

Haka kuma a ranar Talata da dare, sojojin sun bayyana cewa akwai jami’ansu 15 wadanda aka raunata a Gaza a cikin sa’o’i 24, inda sojojin suka ce shida na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai

0230 GMT — Mayakan Hamas sun gwabza da sojojin Isra'ila da suka mamaye titunan Gaza

Mazauna garin Khan Younis sun ba da rahoton ƙazamin faɗan bindigogi a yankunan tsakiya da gabashin birnin na kudancin kasar. / Photo: Reuters

Mayakan gwagwarmayar Hamas da sojojin Isra'ila 'yan mamaya sun yi artabu da musayar wuta da bindigogi a kan titunan birnin na biyu mafi girma a Gaza, kamar yadda mazauna da kuma shaidu suka bayyana.

Mazauna garin Khan Younis sun ba da rahoton ƙazamin faɗan bindigogi a yankunan tsakiya da gabashin birnin na kudancin kasar.

Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce an kashe Falasdinawa 12 a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gida a birnin. Isra'ila ta yi asarar sojoji 132 a fadan da ake a cikin Gaza tun bayan da ta mamaye yankin.

Sabon faɗan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta jinkirta kaɗa ƙuri'a kan yunƙurin kara kai kayan agaji ga yankin Falasdinu da ke fuskantar bala'in jinƙai.

Hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke yi, ya sa yankunan gaɓar tekun sun zama kango, tare da jawo yunwa da rashin matsuguni, ya kuma kashe Falasdinawa kusan 20,000, a cewar jami'an yankin.

2140 GMT — Shugaban Hamas Haniyeh zai tafi Masar don tattaunawa kan kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza

Ziyarar Haniyeh za ta kasance karo na biyu a Masar tun bayan fara yaƙin da Isra'ila ta yi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba. Hoto: OTHERS

Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh na shirin kai ziyara kasar Masar domin tattaunawa kan batun tsagaita wuta a Gaza da kuma yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra'ila, kamar yadda wata majiya da ke kusa da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta bayyana.

Majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, Haniyeh wanda ke zaune a Qatar, zai jagoranci wata babbar tawaga ta Hamas zuwa Masar, inda zai tattauna da shugaban hukumar leƙen asirin Masar Abbas Kamel da ma wasu da daban.

Tattaunawar za ta kasance "a kan dakatar da muguntar wuce gona da iri da yaƙi don shirya yarjejeniyar sakin fursunoni (da) kawo ƙarshen hare-haren da ake yi wa Gaza da aka yi wa ƙawanya", in ji majiyar, bisa sharaɗin sakaya sunansa, saboda ba shi da izinin yin magana game da ziyarar.

A karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda a watan da ya gabata, Qatar ta taimaka wajen sasantawa, tare da samun goyon bayan Masar da Amurka, an sako Isra’ilawa 80 da aka yi garkuwa da su, a madadin Falasdinawa 240 da ke garƙame a gidajen yari na Isra’ila. Amma Isra'ila ta kama dubban Falasdinawa tun ranar 7 ga watan Oktoba.

A cewar majiyar Hamas, tattaunawar da za a yi a Masar za ta mayar da hankali ne kan "isar da kayayyakin jinƙai, da janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza da kuma mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwa da ƙauyukan da ke arewacin kasar".

Ziyarar Haniyeh za ta kasance karo na biyu a Masar tun bayan fara yaƙin da Isra'ila ta yi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, bayan wata ziyarar da ya kai a farkon watan Nuwamba.

2230 GMT — Kungiyar masu ikirarin jihadi ta saki bidiyo na wasu Isra'ilawa biyu da suke rokon a sake su

Rundunar mayakan Al Quds ta Kungiyar Gwagwarmayar Falasdinawa ta masu ikirarin jihadi, Palestinian Islamic Jihad ta saki wani bidiyo a shafin Telegram na wasu Isra'ilawa maza biyu da ake garkuwa da su a Gaza suna rokon a sake su.

Mutanen biyu sun bayyana sunayensu da Gadi Moses da Elad Katsir kuma sun bayyana a wani dan gajeren bidiyo suna neman a ƙara ƙaimi domin su sake haɗuwa da iyalansu.

"Muna mutuwa a tsaitsaye. Muna cikin wani yanayi da ba za mu iya jurewa ba," in ji Moses, ya faɗa yana kallon kyamarar daga wani waje da ba a iya ganewa. Mutanen biyu duk ba su yi aski ba kuma da alama sun rame.

Moses Bayahude ne ɗan kama wuri zauna kuma manomi mai kimanin shekaru 79 da aka kama shi daga Kibbutz a ranar 7 ga Oktoba lokacin da mayakan Hamas suka kai wani samame a kudancin Isra'ila.

Katsir, mai shekaru 47, kuma an dauke shi daga Kibbutz tare da mahaifiyarsa, wanda daga baya aka sake shi. An kashe mahaifinsa, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

#