Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke karbar bakuncin taron sauyin yanayi na wannan shekarar, kuma tana da mahalarta mafi yawa -- wato mutum 4,409, Brazil na da mahalarta 3,081 sai Nijeriya da China da kowaccensu ke da mahalarta 1,411.
Ce-ce-ku-ce ya mamaye taron COP28 na sauyin yanayi da ake yi a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa yayin da ‘yan Nijeriya ke korafi kan dumbin ‘yan kasar da suka halarci taron.
Taron na sauyin yanayi taro ne na shekara-shekara wanda a bana Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke da mahalarta taron mafi yawa inda take da mutum 4,409 sai Brazil mutum 3,081 sai Nijeriya da China masu 1,411.
Wannan dalili ne ya sa ‘yan Nijeriyar da dama musamman a shafukan sada zumunta suka fito suna korafi kan cewa bai kamata gwamnatin Nijeriyar ta dauki nauyin dumbin mutanen nan ba a daidai lokacin da kasar ke fama da matsaloli na matsin tattalin arziki.
Sai dai a sanarwar da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ba ita ta dauki nauyin mutum 1,411 da ke halartar taron ba, inda ta ce akwai mutane da dama da kamfanoni wadanda ba ita ta dauki nauyinsu ba.
Korafin wasu ‘yan Nijeriya
Daga cikin masu yin wannan korafin, har da dan takarar shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar Labour Peter Obi wanda ya yi wa kasar shagube tare da caccakar kasar a kaikace kan wannan mataki.
Ita ma sanarwar da mai magana da yawun Jam’iyyar PDP Debo Ologunagba ya fitar ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta ce asarar kudin kasa ne.
Jam’iyyar ta ce bai kamata gwamnatin Nijeriyar ta kashe irin wadannan kudaden ba a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale na tattalin arziki.
Me gwamnatin Nijeriya ke cewa?
A wata sanarwa da Ma’aikatar Watsa Labarai ta Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa akwai ‘yan kasar da dama da ba Nijeriya ta dauki nauyinsu ba.
Gwamnatin Nijeriyar ta ce daga cikin wadanda suka halarci taron daga kasar akwai shugaban bankin UBA Tony Elumelu da Abdul Samad Rabiu Shugaban BUA da sauran masu kudi ‘yan kasuwa.
Gwamnatin Nijeriyar ta jaddada cewa wadannan ‘yan kasuwan sun taho da ma’aikatansu domin ci gaban kasuwancinsu, kuma suna daga cikin mutum 1,411 daga Nijeriya inda ta ce ba gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyinsu ba.
Daya daga cikin hadiman tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wato Bashir Ahmed ya tabbatar da batun na gwamnatin Nijeriyar inda ya wallafa takardar gayyatar da aka yi masa tare da cewa shi ya dauki nauyin kansa.