Ranar Lahadi ne Juventus ta sallami kocinta Thiago Motta wanda bai cika shekara guda da karɓar aiki a ƙungiyar da a baya ta mamaye ƙwallon ƙafa a Italiya ba.

Abin da ya sa Juventus ta sallami kocinta Thiago Motta

Juventus ta Italiya ta raba gari da kocinta Thiago Motta sakamakon taɓarɓarewa lamura a ƙungiyar da a baya ta mamaye ƙwallon ƙafa a Italiya. Juventus ta zama lami a hannu kocin mai shekaru 42.

Cikin wasanni 29 na kakar Gasar Serie ta bana a Italiya, Juventus ta ci wasa 13, ta yi canjara har sau 13, sannan ta yi rashin nasara sau 3. Sannan ‘yan wasan da ya sayo a bazarar bara sun gaza kawo babban sauyi ga tagomashin ƙungiyar.

Hukuncin korar Motta ta zo ne bayan shan kaye da ci 4-0 a hannun Atalanta, wanda shi ne mafi munin kaye tun 1967 – da kuma rashin nasara da ci 3-0 a Fiorentina, wanda ya sa suke mataki na biyar a teburi.

Zuwan Thiago Motta Juventus a Yunin 2024 a matsayin babban koci ya haifar da ƙaƙƙarfar fata, ganin cewa shekara guda kafin nan, kocin ya yi nasarar kai ƙungiyar Bologna zuwa Gasar Zakarun Turai.

Sai dai a watan jiya, an fitar da Juve daga Gasar Zakarun Turai a hannun PSV Eindhoven, sannan an fitar da su daga Gasar Italian Cup a hannun Empoli, gasar da suka ɗauka shekara ɗaya baya.

Kocin wanda ɗan Italiya ne tsatson Brazil ya yi zaɓin ‘yan wasa da aka soka, musamman ajiye ɗan wasan tsakiya ɗan Serbia, Dusan Vlahovic da ɗan Turkiyya Kenan Yildiz a benci.

A sanarwarta Juventus ta ce, "Kulob ɗinmu na miƙa godiya ga Thiago Motta da duka ma’aikatansa kan ƙwarewarsu, da kuma ƙoƙarin da suka nuna a watannin baya tare da nuna sadaukarwa da mayar da hankali".

Naɗa Tudor

Juventus ta naɗa tsohon ɗan wasanta ɗan asalin Croatia Igor Tudor, wanda ya buga mata wasa 174, kafin ya fara aikin koci. A baya ya riƙe ƙungiyoyi kamar Verona, Marseille da Lazio.

Sanarwar ƙungiyar ta ce, "Juventus na sanar da cewa yanzu Igor Tudor zai jagoranci kulob ɗin, kuma zai karɓi aikin horar da ‘yan wasanmu a karon farko ranar Litinin, 24 ga Maris."

Juventus ta bai wa Tudor aikin nemo mata mataki na huɗu a teburin Serie A, wanda shi ne matakin cancanta damar buga gasar Zakarun Turai, wanda ke da muhimmanci ga samun kuɗin ƙungiyar.

#