Ana binciken zarge-zargen cin zarafi da suka bayyana a kansa a lokuta daban-daban

Yansandan Legas sun gayyaci Fasto Chris Okafor kan zargin fyaɗe

Rundunar ‘yansandan Jihar Legas ta gayyaci babban fasto na cocin Mountain of Liberation and Miracles Ministries, Chris Okafor, domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen aikata fyaɗe a lokuta daban-daban. An umarce shi da ya gabatar da kansa ga Sashen Binciken Laifuka na Jiha (SCID) da ke Panti kafin ƙarfe 10:00 na safiyar Litinin.

Kwamishinan ‘Yansandan jihar, Olohundare Jimoh, ya umarci jami’an SCID su gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen. Rundunar ta ce an riga an bai wa faston takardar gayyata ta hannun lauyansa, kuma ana sa ran zai bayar da cikakken haɗin kai ga masu bincike.

‘Yansandan sun ce an samar da tsaro ga waɗanda ake zargin an ci zarafinsu domin su ba da shaida, tare da tabbatar da cewa za a kare sirrin duk wanda abin ya shafa yayin binciken. Haka kuma sun bukaci duk wanda ke da bayanai ko shaidu kan lamarin da ya kai rahoto ga rundunar.

Binciken ya biyo bayan zarge-zargen da suka bayyana a shafukan sada zumunta a watan Disamba 2025, ciki har da na jarumar Nollywood Doris Ogala, wacce ta yi ikirarin cewa ta taɓa yin alaƙa ta jima’i da faston tun daga shekarar 2017 na tsawon shekaru tara.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 
#