Harin kwanton-ɓauna ya afku ne a yankin Kanam yayin sintirin haɗaka

‘Yanbindiga sun kashe jami’an tsaro da ‘yan bijilanti 20 a Filato

Aƙalla jami’an tsaro da ‘yan bijilanti 20 ne suka mutu bayan da ‘yanbindiga masu ɗauke da manyan makamai suka kai wa tawagar sintiri ta haɗaka harin kwanton-ɓauna a yankin Garga da ke Ƙaramar Hukumar Kanam ta Jihar Filato.

Kungiyar Kanam Development Association (KADA) ta ce mamatan sun haɗa da jami’an tsaro 12 ciki har da manyan jami’an soja biyu, da kuma ‘yan bijilanti takwas da ke taimaka wa jami’an tsaro wajen kare al’ummomin yankin.

Rahotanni sun ce tawagar sintirin na kan hanyarsu ta gudanar da sintiri a ƙauyukan Garga, Kyaram da Gyambau ne a cikin motoci biyu lokacin da ɗaruruwan ‘yanbindiga suka yi musu kwanton-ɓauna a hanyar zuwa Wanka da misalin ƙarfe 2:00 na rana ranar Juma’a.

Bayan harin, an ruwaito cewa ‘yanbindigar sun kutsa cikin al’ummar Kyaram inda suka wawushe dukiyoyi na miliyoyin naira tare da kwashe shanu masu yawa na mazauna yankin.

Kungiyar KADA ta ce ta dade tana gargadin hukumomi kan tabarbarewar tsaro a yankin, inda ta bukaci gwamnatocin ƙaramar hukuma, jiha da ta tarayya su gaggauta ɗaukar matakan dakile karin zubar da jini.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 
#