Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 daga makarantar sakandare a Kebbi

Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 daga makarantar sakandare a Kebbi

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace ɗalibai 25 daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye harabar makarantar.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar Kotarkoshi, ya fitar, ya ce maharan dauke da makamai masu ƙarfi sun kutsa cikin makarantar inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro da ke bakin aiki.

Sanarwar ta ce duk da ƙoƙarin jami’an tsaron, maharan sun haye katangar makarantar sannan suka shiga ɗakunan kwanan ɗalibai inda suka yi awon gaba da su.

Rahoton ya kuma bayyana cewa Hassan Makuku, wanda aka ce mataimakin shugaban makarantar ne, ya rasa ransa yayin harin, yayin da wani Ali Shehu ya samu rauni bayan harbin bindiga ya same shi a hannunsa na dama.

Bayan aukuwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello Muhammad Sani, ya tura jami’an ‘yan sanda na musamman tare da sojoji da ‘yan bijilanti zuwa yankin domin bin sawun maharan.

A halin yanzu tawagar haɗin gwiwa na ci gaba da bincike a hanyoyin da ake zargin maharan suka bi da kuma dazuzzukan da ke kewaye da yankin domin ceto ɗaliban da kuma kamo masu aikata laifin.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da muhallinsu, yana mai tabbatar musu cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 
#