Dollar

42,0958

0.24 %

Euro

48,6520

-0.18 %

Gram Gold

5.413,4200

-0.31 %

Quarter Gold

9.254,6300

0.46 %

Silver

65,8700

-0.26 %

Samamen ya biyo bayan wani rahoto da aka samu ne cewa an yaudari wasu ‘yan kasashen waje aka shigo da su Nijeriya da nufin za a samar musu ayyuka masu kyau, amma da isowarsu sai aka yi garkuwa da su.

‘Yan sandan Nijeriya sun ceto ‘yan kasashen waje 23 da aka yi garkuwa da su

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta yi nasarar ceto wasu ‘yan kasashen waje 23 da aka sace tare da kama mutum 14 da ake zargi da satar mutanen don kudin fansa.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Abujan, Josephine Adeh a wata sanarwa ta ce an gudanar da aikin samamen na leken asiri ne ranar 22 ga watan Oktoban 2025, a Angwan Adamu Ruga Fulani Zone B, Riverside, da ke Ado Mararaba a jihar Nasarawa.

“A wata gagarumar nasara kan masu satar mutane don kudin fansa da masu safarar mutane, jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya sun kama mutum 14 da ake zargi da satar mutane don kudin fansa tare da ceto mutum 23 ‘yan kasashen waje da aka yi garkuwa da su,” in ji sanarwar ‘yan sandan a ranar Jumma’.a

Samamen ya biyo bayan wani rahoto da aka samu ne cewa an yaudari wasu ‘yan kasashen waje aka shigo da su Nijeriya da nufin za a samar musu ayyuka masu kyau, amma da isowarsu sai aka yi garkuwa da su.

Daga nan sai masu satar mutanen suka nemi sai iyalan mutanen sun biya kudin fansa ta hanyar tuntubarsu ta WhatsApp da sauran kafofin intanet.

 ‘Yan sandan Abuja sun ce sakamakon binciken farko ya nuna cewa wani mutum mai suna Abubakar Jigiba ne yake jagorantar gungun masu satar mutanen da ke ayyukansu a
Côte d’Ivoire, Ghana, Mali, da Nijeriya.

Sannan kaninsa Sougule Zoubere ke daukar ma’aikatan da safarar mutane daga Mali zuwa Nijeriya, inda a can ake tsare mutane har sai an biya kudaden fansa.

“Bincike ya nuna cewa an yi safarar wadanda abin ya shafa zuwa kasar ta hanyoyin kan iyaka ba bisa ka’ida ba a cikin tafiya ta tsawon kwanaki uku. Daga baya an tsare su a wani gida mai daki biyu a cikin yanayi na rashin tausayi,” in ji PPRO.

“Ta hanyar amfani da bayanan sirri na dijital da na liken asiri, rundunar Scorpion Squad ta gano maboyar, inda aka gano fiye da mutum 23 da ake garkuwa da su, wadanda suka kunshi maza 14, mata takwas, da yaro daya.

“Amma ba wanda ya ji rauni, sai dai wanda ya sami karamin rauni a kunne kuma an kai shi Asibitin Kasa, Abuja, don neman kulawar likita.”

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#