Rahotanni sun ce wasu gungun mutane ne suka tare ‘yan arewacin ƙasar waɗanda mafarauta ne a garin Uromi da ke ƙaramar hukamar Esan North East ta Jihar Edon, a kan hanyarsu ta tafiya arewa.

‘Kisan gillar’ da aka yi mafarauta ‘yan arewacin Nijeriya a kudu ya ta da hankula a ƙasar

Mummunan kisan gillar da aka yi wa wasu ‘yan arewacin Nijeriya a jihar Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar ya tayar da hankula a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce wasu gungun mutane ne suka tare ‘yan arewacin ƙasar waɗanda mafarauta ne a garin Uromi da ke ƙaramar hukamar Esan North East ta Jihar Edon, a kan hanyarsu ta tafiya arewa.

Tuni Gwamnan Jihar Edo Monday Okpebholo ya bayar da umarnin yin bincike kan kisan mafarautan waɗanda ke tafiya gida don yin bikin ƙaramar sallah.

Gungun mutanen sun tare motar matifyan inda suka ga bindigogin toka irin na mafarauta, sai kawai suka ayyana cewa masu garkuwa da mutane ne.

A cikin wani bidiyo da ya yaɗu a intanet, an ga yadda gungun suka yi wa mafarautan dukan kawo wuƙa sannan suka cinna musu wuta suka ƙona su ƙurmus.

Wannan bidiyo ya ɗaga hankulan al’ummar ƙasar musamman daga arewaci, inda mafi yawa suke kira ga gwamnati da ta yi gaggawar ɗaukar matakin da ya dace.

Wasu kuma sun yi ta zargin gwamnatin da gaza daƙile irin wannan kisan gilla na ɗaukar doka a hannu wanda yake yawan faruwa a Nijeriya.

Allah wadai

Gwamnan Edo Monday Okpebholo ya bayyana lamarin da mummunan abu tare da yin Allah wadai da shi, yana mai shan alwashin zaƙulo masu hannu a ciki da gurfanar da su a gaban shari’a.

Kazalika cikin waɗanda suka yi tur da lamarin zuwa har da ɗan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwanso.

Gwamnan wanda ya yi magana a Uromi ta bakin Babban Jami’in Tsaro (CSO) da gidan gwamnati da SP Solomon Osaghale, ya ce ya je ne domin sanin irin barnar da aka yi da kuma tabbatar da cewa an gudanar da bincike don tabbatar da adalci da hana sake aukuwar lamarin.

Ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa wadanda aka kashen sun shiga wata babbar mota ta haya ne kuma jami’an tsaron yankin suka tare su inda bayan binciken motar suka gano wasu bindigogi, lamarin da ya kai jama’a da ke kusa da wurin suka far musu.

Ya yi gargadin cewa babu wanda ke da hakkin ya kashe wani mutum, yana mai jaddada cewa irin kisan gillar da aka yi ya kawo damuwa ga Gwamnan.

“Ina mai tabbatar muku da cewa mutanen da ke da hannu a wannan harin ba za su ci banza ba, saboda mai girma gwamna ya umurci kwamishinan ‘yan sanda da ya kaddamar da cikakken bincike kan lamarin.

"Kamar yadda nake magana yanzu, an kama sama da mutane hudu da hannu a cikin wannan mummunan lamari," in ji shi.

Sai dai ya yi kira da a kwantar da hankula yayin da yake ba wa mazauna garin Uromi, musamman al’ummar Hausawa mazauna yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, domin an tura jami’an ‘yan sandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

#