Publication : 12 February 2026
Update : 12 February 2026
Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Iran kan shirin nukiliya
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba a cim ma wani takamaiman abu ba yayin ganawarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, sai dai ya nanata cewa za a ci gaba da tattaunawa da Iran domin duba yiwuwar ƙulla wata yarjejeniya. TRT Hausa
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social bayan ganawar da suka yi a Fadar White House, inda ya ce abin da ya fi so shi ne a samu yarjejeniya ta diflomasiyya da Iran, amma idan hakan bai yiwu ba, dole a fuskanci sakamakon. TRT Hausa
Ya ce sun kuma tattauna kan ci-gaban da ake samu a Gaza da kuma halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki baki ɗaya. TRT Hausa
A nasa ɓangaren, ofishin Netanyahu ya ce Firaministan Isra’ila ya jaddada batun tsaron Isra’ila yayin tattaunawar da Trump kan shirin nukiliyar Iran. TRT Hausa
Ganawar, wacce ita ce ta bakwai tsakanin shugabannin biyu tun bayan Trump ya koma mulki, an yi ta ne a ɓoye, inda aka hana manema labarai shiga, kuma Netanyahu ya bar fadar ba tare da faretin ban-girman da aka saba yi wa baƙi ba. TRT Hausa
Washington da Tehran sun sake soma tattaunawar nukiliya a makon jiya a Oman, bayan da aka dakatar da su sakamakon hare-haren sama da Amurka ta kai kan wasu wuraren nukiliyar Iran a lokacin rikicin kwanaki 12 da ya auku a bara. TRT Hausa
Anthrax outbreak kills 46 hippos and eight elephants in Zambia
An anthrax outbreak in northern Zambia has killed 46 hippos, eight elephants, five buffaloes and a crocodile, while 12 people have been infected with the disease.
Nearly 3,400 people die of Ebola in DRC since mid-May 2026
The number of confirmed Ebola cases in the current outbreak in the Democratic Republic of Congo has crossed 7,000 since mid-May, according to official data.
Uganda's ex-military intelligence officer extradited to US to face arms smuggling charges
A former confidant of Uganda's army chief has been extradited to the United States for allegedly plotting to provide weapons to Mexican drug cartels.
Most Read
All rights reserved. Newstimetr © 2023