Dollar

42,2463

0.06 %

Euro

49,0110

0.13 %

Gram Gold

5.687,0500

1.44 %

Quarter Gold

9.512,1700

-0.01 %

Silver

71,9900

3.49 %

Badaru ya fadi hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai na Bikin Ranar Tunawa da Dakarun Soji na 2026 da aka yi a ranar Laraba a Abuja.

Za mu bai wa kowane jami'in soja da ke bakin aikinsa kariya  - Ministan Tsaron Nijeriya

Ministan Tsaron NIjeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce gwamnatin tarayya za ta kare duk wani jami’in rundunar tsaron kasar da ke aikinsa bisa doka da oda.

Badaru ya fadi hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai na Bikin Ranar Tunawa da Dakarun Soji na 2026 da aka yi a ranar Laraba a Abuja.

Minista Badaru ya yi wadannan kalamai ne bayan wata sa’insar da ta faru a ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da wani sojan ruwa, Laftanal Kanal A.M Yerima a kan wani fili a Abuja.

'Yan Nijeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu sakamakon sa-in-sar da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya yi da wani matashin soja mai suna A.M. Yerima a yayin duba wani fili da ya yi zargin cewa ba a bi doka wajen mallakarsa ba.

Taƙaddamar ta fara ne a lokacin da Minista Wike ya yi tattaki da kansa zuwa filin, wanda mallakin wani tsohon babban hafsan sojin ruwa ne da aka jibge sojoji a cikinsa.

Wike ya nuna ɓacin ransa bayan sojan ya hana shi shiga filin, inda ya riƙa zagin sojan, matakin da wasu ke ganin bai dace ba.

Da yake magana kan lamarin, Badaru ya ce Ma’aikatar Tsaro tana sane da lamarin kuma za ta tabbatar da cewa an bai wa dukkan jami’ai kariya a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

“A ma’aikatar nan, dama cikin rundunar soji, za mu kare dukkan jami’ai da ke bakin aiki a ko yaushe,” ya ce.

“Muna nazarin wannan batun, kuma ina tabbatar muku cewa duk wani jami'i da yake aikinsa bisa ka'ida za a ba shi kariya. Ba za mu bari wani abu ya faru da shi ba matukar a kan aikinsa yake kuma yana yin aikin yadda ya kamata.”

Sai dai ministan bai fayyace bayani a kan binciken da ake yi kan lamarin ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#