Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Daraktan WHO na yankin Afirka, Dr Mohamed Janabi a wani sako na Ranar Ciwon Siga ta Duniya ya ce nahiyar tana ganin ta’azzarar cutar sikari saboda tsarin yanayin rayuwa mara kyau da karuwar mummunar kiba da teba da kuma rashin tsarin kiwon lafiya mai

WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu fama da ciwon siga a fadin Afirka, tana mai kira da a gaggauta yin kokarin magance wannan gagarumar matsala ta lafiya da ke yi wa miliyoyin rayuka barazana.

Daraktan WHO na yankin Afirka, Dr Mohamed Janabi a wani sako na Ranar Ciwon Siga ta Duniya ya ce nahiyar tana ganin ta’azzarar cutar sikari ne saboda tsarin yanayin rayuwa mara kyau da karuwar mummunar kiba da teba da kuma rashin tsarin kiwon lafiya mai kyau.

Ya fayyace cewa akwai mutum fiye da miliyan 24 a Afirka da a yanzu haka suke fama da ciwon siga, wasu alkaluma da ake hasashen za su kai miliyan 60 nan da shekarar 2050, tare da gargadin cewa ba a ma gano rabin masu fama da cutar ba, lamarin da ke jawo mace-macen da za a iya kare afkuwarsu.

Dr Janabi ya ce dole ne gwamnatocin Afirka su karfafa tsarin kiwon lafiyarsu don tabbatar da gano cutar da wuri, da magance ta da kyau da samun kulawa, yana mai cewa idan ba a gano masu dauke da cutar ba, hakan ka iya dakushe tattalin arziki da jawo koma-baya.

Ya fayyace cewa kasashe irin su Ghana da Uganda tuni suka sanya ciwon siga da cututtukan zuciya a cikin tsarin lafiya na matakin farko karkashin shirin WHO Global Diabetes Compact na 2024.

Daraktan WHO na shiyyar Afirkan ya nemi kasashe da zu inganta tsarin lafiya a fannin abinci da motsa jiki da samar da magani a bisa farashi mai rangwame ga kowa, yana mai jaddada cewa gano cutar da wuri da kuma yin sauye-sauye a tsarin rayuwa yana iya rage barazanar kamuwa da cutar sosai.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#