Gwamnatin Saudiyya ta ce 'yan Nijeriya da aka hana su shiga kasar domin yin aikin Umrah sun keta dokar mallakar biza.

Umrah: Saudiyya ta bayyana dalilin da ya sa ta soke bizar 'yan Nijeriya 264  bayan sun isa Jeddah

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa ta soke bizar 'yan Nijeriya 264 da suka isa Jeddah daga jihohin Legas da Kano a ranar Lahadi ne saboda ba su cika ka'ida ba.

Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da maraice.

Batun hana ‘yan Nijeriya da suka isa Jeddah a jirgin Air Peace sauka a kasar Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan intanet har ta kai ga gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin gudanar da bincike a kansa.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Nijeriya suka kulla wasu yarjejeniyoyin kasuwanci da Saudiyya, bayan ziyartar taron Kasuwanci na Saudiyya da kasashen Afirka da aka yi a birnin Riyadh.

'Tsarin dokar Saudiyya'

Sanarwar da ofishin jakadancin na Saudiyya ya fitar ta ce an "fasinjojin da aka hana shiga" Saudiyya sannan aka "koma da su" kasarsu "ba su cika sharudan shiga Masarautar ba, saboda sun bayar da bayanan da ba daidai ba ne domin neman bizar ba ba ita ya kamata su karba."

Sanarwar ta kara da cewa an gano hakan ne bayan sun isa Jeddah, abin da ya sa aka mayar da su Nijeriya.

#