Michael Eneramo, mai shekara 40, ya faɗi a cikin fili a lokacin da ake buga wasan sada zamunta a ranar Juma'a, kamar yadda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya ta bayyana.

Tsohon ɗanwasan Nijeriya Eneramo ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin wasan sada zumunta

Tsohon ɗanwasan gaba na Nijeriya, Michael Eneramo, ya mutu bayan ya faɗi a fili yayin wasan sada zumunta ranar Juma'a.

Alamu sun nuna cewa, Eneramo mai shekaru 40, ya gamu da bugun zuciya mintuna biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan sada zumuntar,' in ji Hukumar Kwallon Kafar ta Najeriya, tana ambato rahotannin farko-farko.

Eneramo ya buga wasa gaba daya kafin a tafi hutun rabin lokaci a Ungwan Yelwa da ke Kaduna, a safiyar Juma'a.

'Wannan abin tashin hankali ne matuƙa. Ba ni da kalmomin da zan iya bayyanawa a wannan lokaci,' in ji Sakatare Janar na NFF, Mohammed Sanusi.

Eneramo ya buga wa Nijeriya wasanni 10 bayan ya ƙi karɓar damar wakiltar Tunisiya, inda ya yi fice a kulob-kulob kuma yake duba yiwuwar samun shaidar zama ɗan ƙasar.

Magoya bayan ƙungiyar Espérance Sportive ta Tunis sun sanya masa suna 'The Tank', kuma, a cewar NFF, ya taimaka wa ƙungiyar wajen samun wasu kofuna. Haka kuma ya buga wasa a Turkiyya a ƙungiyoyin Sivasspor, Beşiktaş da Başakşehir, da sauran su.

Eneramo ya fara wakiltar Najeriya a wasan sada zumunta da Jamaica a Fabrairun 2009, sannan ya zura ƙwallonsa ta farko a wasan ƙasa da ƙasa a karawar da suka yi da Ireland watanni uku bayan wasan Jamaica, wanda shi ma wasa ne na sada zumunta.

#