Shugaban Amurka ya nuna cewa ana gab da tsayar da matsaya kan daukar karin matakan soji ko kuma cim ma yarjejeniya da Tehran.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole ne ya yanke shawara kan ko zai ƙara ci gaba da yaƙi da Iran ko kuma ya cim ma yarjejeniya, yana mai nuna cewa yana dab da yanke shawara ba tare da bayyana matakin da zai ɗauka na gaba ba.
Da manema labarai suka tambaye shi yadda yake shirin ɗaukar mataki kan jami'an Iran, Trump ya amsa da cewa: "Wataƙila a ruguza su."
"Dole ne mu yanke wannan shawara: Mu ruguza su ko mu cim ma yarjejeniya," in ji Trump, yana mai ƙari da cewa "Amma lokaci yana zuwa. Zai ƙare nan ba da jimawa ba, ko ta halin ƙaƙa."
Shugaban Amurka ya nuna cewa ana gab ɗaukar matsaya kan ƙarin matakan soja ko kuma cim ma yarjejeniya da Tehran.
Cikin ‘yan makonnin nan, Trump ya sha faɗin cewa yana nazari kan ɗaukar ƙarin matakan soja ko kuma ya cim ma yarjejeniyar da Tehran.
Kazalika Shugaban na Amurka ya musanta rahotannin kafofin watsa labarai na baya bayan nan da ke cewa yana son ba da sassaucin takunkumin tattalin arziki da kuma sakin kuɗaɗen da aka hana amfani da su na Iran don musanya da shirin nukiliyarta.
"Wuce-gona-da-iri"
Kafofin watsa labaran Amurka Axios da CNN sun ruwaito a ranar Litinin cewa shugaban Amurka ya ba Iran sassaucin takunkumi da kuma sakin kuɗaɗen da aka dakatar, yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙara zafi.
"Axios ya fitar da wani labari da ke cewa 'Trump' ya bayar da sassauci ga takunkumi da kuma kudaden da aka riƙe ga Iran. Wannan ba gaskiya ba ne. Ban ba su KOMAI BA!" kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social.
A ƙarshen mako, shugaban Amurka ya yi watsi da shawarar Iran wadda ta mayar da hankali kan sassauta rikicin da sake buɗe Mashigar Hormuz, yana mai bayyana buƙatar Tehran da wanda "ba za a yarda da shi ba" a yanayin yakin Iran na watanni bakwai.
Trump ya fada a karshen makon nan cewa, yana sa ran karin tattaunawa da Tehran, kana ya yi ikirarin cewa jami'an Iran sun "wuce-gona-da-iri" a lokacin tattaunawarsu ta baya.

