Shuwagabannin gwamnatoci da kasuwanci a Afirka suna hallara a masar ranar Asaabar domin taron Afirk na farko na Alamein, wanda ke mayar da hankali kan cinikayya da zuba jari.

Shugabannin Afirka sun taru a Masar domin taron cinikayya

Shuwagabannin gwamnatoci da kasuwancin Afirka sun hallara a Masar ranar Asabar domin taron Afirka na farko na Alamein, da ya mayar da hankali kan cinikayya da zuba jari da hadin kai na tattalin arziki a faɗin nahiyar.

Shugaban Masar Abdel Fattah Al Sisi ne ya buɗe taron a New Alamein, wani birni a gaɓar tekun meditereniyan da ke arewacin Masar. Taron tare da taron manyan jami;an Ƙungiyar Tarayyar Afirka ana yin su ne daga ranar 2 zuwa ranar4 ga watan Oktoba.

Shuwagabannin da suka hallara a Masar sun haɗa da Evariste Ndayishimiye na Burundi da Joao Lurenco na Angola da John Mahama na Ghana da kuma Hassan Sheikh Mohamud na Somalia. Shugaban kwamitin mulkin Libya Mohamed Al Menfi da mataimakin shugaban ƙasar Tanzania Deogratius Ndejembi da mataimakiyar shugaban ƙasar Uganda Jessica Alupo sun halarci taron.

Kazalika shugaban Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf ya tara massu tsare-tsare na Afirka da na ƙtare da masu zuba jari da hukumomin tattalin arziki. Taron na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatoci ke neman zurfafa cinikayya tsakanin Afirka da kuma zuba jari a ƙarƙashin yarjejeniyar AfCFTA ta ‘yancin cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka.

An yi kira da cinikayya a 'aikace' tsakanin Afirka

Sisi ya yi kira da ƙrfafa dangantaka tsakanin kamfanoni da kuma inganta damar samun bayanai game da kasuwannin da kuma matakai a aikace don inganta cinikayya a cikin Afirka. Ya kuma bayyana zaman lafiya da hukumomi masu ƙarfi a matsayin ginshiƙan zuba jari da ci-gaba.

Babban jami;in hukumar ƙungiyar haɗin kan Afirka Youssouf ya yi kira ga ƙasashe su sauya burin ci-gaba zuwa ayyuka da aka tsara da kyau tare da iakata da kuɗin da ya dace. Shugaban Burundi President Evariste Ndayishimiye, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU, ya yi kira da a samar da ƙarin hadin kai tsakanin gwamnatoci da masu zuba jari da kamfanoni domin gina ayyuka da za a iya dogara a kais.

Shugaban bankin shigowa da fitar da kayayyaki na Afirka (Afreximbank) George Elombi ya jaddada rawar da bankuna ke takawa wajen tallafa wa cinikayya da kuma mayar da martani girgizar tattalin arziki.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ya yi kira ga ƙarin daidaita dokoki da ƙa’idoji da hnayoyin biyan kuɗaɗe da tsare-tsaren kna iyakoki domin rage tsadar cinikayya da kuma tallafa wa gina masana’antu.

Mayar da hankali kna fannoni daban daban

Taron ya mayar da hankali ne kan ababen more rayuwa da makamshi da sauya lamurra ta dijital da muhimman ma’adinai da kuma ƙera abubuwa a yanki.

Waɗanda suka tsara taron suna tsammanin zaman ya taimaka wajen inganta ayyuka mafi muhimmanci domin samar da kuɗi da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki a faɗin Afirka.

#