'Yan tawayen M23 sun yi iƙirarin ƙwace birnin Goma mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo.
Ɗaruruwan ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo sun tsere zuwa maƙociyar ƙasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo ɗin suka “miƙa wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan tawayen M23 sun ƙwace iko da birnin Goma mai muhimmanci a Kongo.
Wasu bidiyoyi da gidan Radiyo da Talabijin na Rwanda ya wallafa a shafin X, sun nuna wani abin da ke nuna kamar sojoji ne, wasu cikin kayan sarki, suna miƙa makamai ga jami’an tsaron Rwanda, bayan tsallakawa gabashin ƙasar mai maƙotaka ta kan babbar iyakar ƙasar a yankin Rubavu na Rwanda.
Lamarin na baya-bayan nan ya zo ne sa’o’i bayan ‘yan tawayen M23 sun yi iƙirarin shiga Goma, abin da ya tilatsa wa mutane tsarewa daga birnin.
‘Yan tawayen na M23, waɗanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda, sun zafafa hare-hare a gabashin Kongo a makon jiya, inda suka ƙwace muhimman birane.
Sai dai Shugaban Rwanda Paul Kagame ya sha musanta zargin cewa yana goyon bayan ‘yan tawayen.
Mummunan fasa gidan yari a Goma
An fuskanci wani gagarumin fasa gidan yari da safiyar Litinin a birnin Goma na Kongo da aka yi wa kofar-rago, sa’o’i bayan mayaƙa daga ƙungiyar ‘yan tawayen ta M23 sun shiga birnin, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa AFP.
An yi wa gidan yarin wanda yake da fursunoni kimanin 3,000 raga-raga, bayan ɓalla gidan yarin, abin da ya haifar da “mace-mace”, a cewar majiyoyin, ba tare da bayar da wani ƙarin bayani ba.
Ana iya ganin fursounonin da suke tserewa a titunan da suke kusa da yankin, kamar yadda wani wakilin AFP ya bayyana.
Shugabannin ƙasashen Gabashin Afirka za su yi taron gaggawa
Shugaban Kenya William Ruto, wanda yake shugabancin Ƙasashen Gabashin Afirka ya sanar a ranar Lahadi cewa, ƙungiyar za ta gudanar da wani taro na musamman a cikin sa’o’i 48 don tunkarar rikicin da yake yaɗuwa a Jamhuriyar Dimukuraɗiyar Kongo.
Ruto ya tabbatar da cewa tun da farko ya tattauna da Shugaban DRC Kongo Felix Tshisekedi da Shugaban Rwanda Paul Kagame, waɗanda dukkansu suka amince za su halarci taron.
A wata sanarwa da ofishin shugaban ƙasa ya fitar a Kenya, Ruto ya bayyana damuwa kan yadda lamarin yake ƙara taɓarɓarewa a yankin, abin da ya haifar da mummunan yanayi da kuma jefa jama’a cikin mawuyacin hali.
Ya ce rikicin a Kongo ya haifar da munanan ayyukan soja, da rufe filin jirgin sama na Goma, abin da ya ƙara jefa jama’ar yankin cikin mawuyacin hali.
An rufe iyakar DRC da Rwanda
An rufa iyakar Rwanda da DRC kusa da birnin Goma da aka yi wa ƙofar-rago a ranar Litinin, a cewar shaidu, ‘yan sa’o’i bayan ‘yan tawaye sun shiga babban birnin ƙasar Kongo da ke Gabashin Afirka.
“Babu mai shiga babu mai fita, in ban da tsirarun ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da iyalensu da suka fice da safen nan,” kamar yadda wani ma’aikacin agaji a kan iyakar ƙasashen biyu ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.