Rabon kuɗin na daga cikin wani shiri da aka ce an tsara shi domin daƙile wata zanga-zanga da aka shirya yi kan mutuwar ma’aikatan haƙar ma’adinai 37 da suka mutu a hannun jami’an tsaro kimanin makonni biyu da suka gabata.

Nijeriya: Mutane uku sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin kuɗi a Jihar Neja

Akalla mata uku sun mutu bayan turmutsitsi da ya faru yayin rabon tallafin kuɗi a jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya, a cewar wani ma’aikacin lafiya da ya yi magana da kamfanin dillancin labaran AFP.

Dubban mutane ne suka taru a daren Talata a gidan gwamnatin jihar Neja, inda ake rabon naira 10,000, kwatankwacin dala 7.50, ga kowane mutum.

Rabon kuɗin na daga cikin wani shiri da aka ce an tsara shi domin daƙile wata zanga-zanga da aka shirya yi kan mutuwar ma’aikatan haƙar ma’adinai 37 da suka mutu a hannun jami’an tsaro kimanin makonni biyu da suka gabata.

Wani rahoton tsaro da aka shirya wa Majalisar Dinkin Duniya, wanda AFP ta gani, ya ce an shirya rabon kuɗin ne a wani ɓangare domin hana zanga-zangar.

Al’amarin mutuwar ma’aikatan haƙar ma’adinan, wadanda rahotanni suka ce sun shake ne a cikin wani ɗaki mai cunkoso da rashin isasshen iska, ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar Neja cikin makonnin baya-bayan nan.

Wani jami’in jinya a Babban Asibitin Minna da ke ƙarƙashin gwamnatin jihar ya ce an kawo mutane shida da suka jikkata tare da gawarwaki uku.

Ya ce dukkan mutanen da suka mutu mata ne, amma ya nemi a sakaya sunansa saboda fargabar fuskantar hukunci.

Sai dai rahoton tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya ce adadin mutanen da suka mutu ya kai biyar.

Kakakin ’yansandan jihar ya ce har yanzu hukumomi na tattara bayanai kan abin da ya faru.

Wani mazaunin yankin, Yusuf Abubakar Bawa, ya ce ’yarsa mai shekaru 15 ta jikkata a turmutsitsin, kuma tana cikin suma.

Matsin tattalin arziki

Nijeriya na fama da matsanancin tsadar rayuwa, yayin da matsalolin tattalin arziki na tsawon shekaru suka jefa miliyoyin mutane cikin talauci.

Hauhawar farashin kayan abinci ta ƙaru sosai tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi a shekarar 2023, da kuma matakin sassauta darajar naira, matakan da masana tattalin arziki suka ce sun daɗe ana buƙatarsu, amma suka haifar da tsananin wahala ga jama’a.

Hauhawar farashin kayayyaki ta haura kashi 30 cikin 100 a mafi tsanani lokacin matsalar tsadar rayuwa, ko da yake daga baya ta ragu zuwa sama da kashi 15 cikin 100 a watan Agusta.

A cewar Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), kashi 63 cikin 100 na al’ummar Nijeriya na rayuwa a ƙarƙashin layin talauci.

Turmutsitsi yayin rabon tallafi

Turmutsitsi mai haddasa asarar rayuka yayin rabon kuɗi ko kayan tallafi ya sha faruwa a Nijeriya.

A watan Disamba 2024, yara 35 sun mutu sakamakon turmutsitsi a wani bikin Kirsimeti a birnin Ibadan da ke kudu maso yammacin ƙasar.

A watan Maris na wannan shekarar, mata 17 sun mutu a turmutsitsin rabon kuɗi a jihar Bauchi. Hakan ya faru kwanaki kaɗan bayan ɗalibai biyu sun mutu a wani turmutsitsi a harabar jami’a a jihar Nasarawa.

A shekarar 2021, rabon takardun samun abinci ga mutanen da rikicin ’yan ta’adda ya raba da muhallansu a Monguno, jihar Borno, ya haddasa turmutsitsi mai kisa.

A watan Afrilun 2020 kuma, wani rabon tallafi kusa da kan iyakar Nijeriya da Kamaru ya haddasa turmutsitsi da ya kashe akalla mata da yara biyar.

#